Minista: An Kammala Binciken Balle Magarkamar Kuje, Sai Dai ba Zamu Yayata ba

Minista: An Kammala Binciken Balle Magarkamar Kuje, Sai Dai ba Zamu Yayata ba

  • Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya sanar da cewa hukumomi sun kammala bincike tsaf kan farmakin da ‘yan ta’adda suka kai gidan yarin Kuje
  • Aregbesola wanda ya sanar da hakan a wani taro da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta shirya, yace ba za a fitarwa da ‘yan kasa sakamakon ba
  • Ministan ya jaddada cewa ‘daftarin tsaro’ ne sakamakon binciken, don haka babu wanda zai sani illa iyaka hukumomin da hakan ya shafa

FCT, Abuja - Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida yace an kammala bincike kan farmakin da ‘yan ta’adda suka kai gidan gyaran hali na Kuje dake babban birnin tarayya, jaridar TheCable ta rahoto.

Farmakin Kuje
Minista: An Kammala Binciken Balle Magarkamar Kuje, Sai Dai ba Zamu Yayata ba. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Aregbesola ya tabbatar da hakan a ranar Talata a Abuja a wani taro da ma’aikatar yada labarai da al’adu suka shirya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Gama Bincike, Ta Gano Mutanen da Suka Kitsa da Ɗaukar Nauyin Fashin Gidan Yarin Kuje

A watan Yuli, ‘yan bindiga sun kai hari magarkamar wanda hakan yasa daruruwan mazauna gidan suka arce har da wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne.

Daftarin Tsaro ne, Minista

Jaridar 21st Century Chronicles ta rahoto cewa, a yayin karin bayani kan binciken farmakin, ministan harkokin cikin gida yace ba za a bayar da bayanin ga jama’a ba saboda “daftarin tsaro ne”.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Har yanzu daftarin tsaro ne.”

- Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto yace.

Aregbesola ya kara da cewa mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi matukar kokari wurin yaki da ta’addanci.

“A 2015, ‘yan ta’addan suna rike da wasu kananan hukumomi a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.”

- Yace.

“Amma a yanzu da muke magana, duk an fatattake su. Tabbas akwai kalubale a nan da can, amma babu wata kasa da take zaune babu kalubale.”

Kara karanta wannan

'Yan Daba Sun Kai Farmaki Wurin Gangamin Yakin Neman Zaben Atiku a Gombe, Sun Yi Ɓarna

Ministan ya kara da cewa, hukumar NSCDC tayi aiki tukuru wurin tabbatar da cewa ta bayar da gudumawarta a fannin tsaro a fadin kasar nan.

“Hukumar ta shiga tayi ruwa da tsaki wurin bai wa kadarori da rayukan ‘yan Najeriya kariya, ballantana a manyan hanyoyin dake fadin kasar nan.”

- Yace.

Harin magarkamar Kuje: Sama da Fursunoni 300 sun arce

A labari na daban, a watan Yulin 2022 ne wasu ‘yan ta’adda suka kai farmaki gidan yarin Kuje.

Bayan budewa jami’an tsaro wuta da suka yi, an gano cewa sun saki fursononi sama da 300.

Asali: Legit.ng

Online view pixel