Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Majalisa A Hanyarsa Na Zuwa Ganin Wakilan Akwatin Zabe
- Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun yi awon gaba da dan takarar majalisa na jam'iyyar APGA, Honarabul Nduka Anyanwu
- Maharan sun tare shi a hanyarsa na zuwa garin Ahiazu don ganawa da wakilan jam'iyyarsa su tattauna batutuwa gabanin zabe a cewar majiya
- An yi kira ga duk wani ko wata da ke da bayani da zai taimaka a ceto Anywanwu ya taimaka ya kai wa yan sanda mafi kusa da shi rahoto
Jihar Imo - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace dan takarar majalisar na mazabar Ahiazu, Honarabul Nduka Anyanwu.
An sace Anyanwu ne a ranar Talata da safe a hanyarsa na zuwa karkare shirye-shirye da tare da wakilansa na akwatin zabe wato ajen a Ahiazu, The Nation ta rahoto.
An yi kira ga al'umma su taimaka wa yan sanda da bayanai don ceto Anyawu
Wasu majiyoyi na kusa da jam'iyyar sun ce yan bindigan sun tare dan takarar na APGA na a hanyarsa na zuwa ganin ajen dinsa, rahoton The Sun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyar ta ce:
"Muna kira ga hukumomin tsaro su bi sahunsu su gano shi. Muna kira ga al'umma duk wani mai bayani da zai taimaka a gano shi ya sanar da ofishin yan sanda mafi kusa.
"Abin ya faru a yau misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata, 22 ga watan Nuwamban 2022."
A cewar majiyar, ana can ana kokarin ganin yadda za a ceto shi.
Yan Fashin Daji Sun Sace Babban Dan Sanda A Jihar Arewacin Najeriya
Yan fashin daji sun sace wani babban jami'in dan sanda mai suna Abdulmumini Yusuf a daren ranar Talata a garin Ogidi da ke karamar hukumar Ilori ta Yamma a Jihar Kwara.
Wahala Mai Tsanani Na Jiran Yan Najeriya Idan Suka Ki Zabar Peter Obi, Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Kasa
Abdulmumini wanda aka fi sani da "Emirate No 1" a unguwar, mataimakin sufritanda ne da ke aiki a rundunar Ilorin, kamar yadda bayanai da aka tattaro suka nuna.
Majiyoyi sun ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata yayin da ya ke dab da shiga gidansa a Ogidi bayan dawowa daga aiki.
Majiyoyi sun shaidawa jaridar Punch Metro a ranar Laraba a Ilorin cewa kwamishinan yan sanda, Paul Odama, ya kai ziyara unguwar bayan afkuwar lamarin.
Asali: Legit.ng