Albishirin ku matafiya: Ana gab da kammala aikin fadada titin Kano zuwa Maiduguri

Albishirin ku matafiya: Ana gab da kammala aikin fadada titin Kano zuwa Maiduguri

- Bangare daya na hanyar Kano zuwa Maiduguri, ya kai kashi 55 na gamawa, shekara 12 bayan bayar a aikinta ga dan kwangilar

- Engr Hungushi ya bayar da tabbacin cewa, idan har aka cigaba da biya, kuma sauran abubuwa na tafiya kamar yanda aka tsara, za’a gama aikin zuwa karshen shekarar 2018

- An bayar da kwangilar aikin ne akan kudi N37bn wanda daga baya aka mayar dashi N55bn

Bangare daya na aikin raba hanya ta Kano zuwa Maiduguri, mai tsawon 101km, wadda ke a jihohin Kano da Katsina, a Arewa maso Yamma ta kai kasha 55 na gamawa, shekaru 12 bayan bayar da ita ga dan kwangilar. An bayyana hakan ne ga kungiyar tarayya tare da hukumar Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje, lokacin da suka kai ziyara a wurin da ake gudanar da aikin, don ganin inda aikin ya tsaya.

Albishirin ku matafiya: An kusa kamalla aikin fadada titin Kano zuwa Maiduguri
Albishirin ku matafiya: An kusa kamalla aikin fadada titin Kano zuwa Maiduguri

Don sanin dalilin jimawar aikin kafin ya kawo wannan matsayi, babban mai kula da aikin, Engr Roy Hungushi yace, rashin kudi duk shine ya janyo nawar aikin da kuma matsalar tsaro a wannan lokaci duk sune suka janyo hakan. Amma ya bayyana godiya ga Ubangiji game da kirkire-kirkiren shugaban kasa. Tunda aka kirkiro kungiyar SUKUK ana biyanmu, shiyasa kake ganin aikin na tafiya ta kowane bangare, inji Engr Hungushi.

KU KARANTA: Za muyi amfani da karfin bindiga wajen ragargazar Boko Haram - Buhari

A lokacin ziyarar, ayyukan na tafiya a tare a kowane bangare da sukeyi. Engr Hungushi, ya tabbatar da cewa indai za’a cigaba da biya kuma abubuwa sun tafi kamar yanda aka tsara, toh za’a gama aikin zuwa karshen shekarar 2018. Hanyar ta Kano zuwa Maiduguri an bayar da kwangilar aikinta a ranar 28, ga watan Satumba, 2006, wanda aikin ya fara a watan Oktoba, 2006. An bayar da ita akan kudi N37bn, amma daga baya aka mayar dashi zuwa N55bn.

Lokacin gamawa na asali shine 11 ga watan Fabrairu, 2010 amma aka karashi sau uku, inda ya koma 31 ga watan Disamba, 2018. Hanyar ta Kano zuwa Maiduguri ta kai nisan 500km, tana daya daga cikin hanyoyi 25 da kungiyar SUKUK ke daukar nauyi. Bangare 2,3,4,5 wadanda duk sun fuskanci koma baya saboda rashin kudi da rashin tsaro, wanda ‘yan kwangila dayawa ne ke aikin daga Arewa maso Gabas. Lokacin ziyarar ‘yan kungiyar sun tarar da ma’aikata suna aiki a kowane bangare na duka hanyoyin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164