Don Samun Zaman Lafiya: Mutanen Zamfara Na Hada N20m Za Su Kaiwa Bello Turji Saboda Ya Daina Farmakarsu

Don Samun Zaman Lafiya: Mutanen Zamfara Na Hada N20m Za Su Kaiwa Bello Turji Saboda Ya Daina Farmakarsu

  • Al'ummar garin Gidan Goga da ke jihar Zamfara sun tashi tsaye domin kwatarwa kansu yanci daga wajen yan ta'adda
  • A kokarinsu na ganin zaman lafiya ya dawo a yankinsu, mutanen garin da ke karamar hukumar Maradun suna neman sulhu da Bello Turji
  • Yanzu haka suna tara kudi naira miliyan 20 zasu kaiwa shugaban kungiyar ta'addancin domin ya sarara masu

Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara za su tara kudi naira miliyan 20 don baiwa kasurgumin shugaban yan bindiga, Bello Turji.

Kamar yadda majiya ta bayyana, mutanen Gidan Goga za su biya wannan kudi ne don kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kubutar da garinsu daga harin Turji, Sahara Reporters ta rahoto.

Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani Turji, ya kasance kasurgumin dan ta’adda kuma shugaban yan bindiga da ke kai hare-hare a jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Zamfara, Sokoto da Neja.

Kara karanta wannan

Sojin sama sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai

Turji
Don Samun Zaman Lafiya: Mutanen Zamfara Na Hada N20m Za Su Kaiwa Bello Turji Saboda Ya Daina Farmakarsu Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ana zargin Turji mai shekaru 28 da jagorantar harin da yan bindiga suka kai jihar Zamfara daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Janairu 2022 inda aka yiwa mutum fiye da 200 da suka hada da mata da yara kisan kiyashi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin mazauna yankin na tara kudaden

Wani mazaunin yankin ya fadama Sahara Reporters cewa:

"Mutanen garin na tara kudi naira miliyan 20 don su ba Bello Turji saboda a kulla yarjejeniyar zaman lafiya da shi don kada a sake kai hare-hare nan."

Har ila yau, wani mazaunin yankin ya sake sanar da jaridar cewa:

“Al’ummar garin na fatan wannan zai kawo karshen hare-hare.

Turji ya rungumi zaman lafiya, Gwamnatin Zamfara

Sai dai kuma, a watan Agustan wannan shekarar ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewar Turji ya rungumi shirinta na zaman lafiya da daukar alkawarin yin maganin kungiyoyin yan ta’adda a yankin.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Bindiga Karkashin Jagorancin Dankarami Sun Sace Mutum 44 a Kanwa dake Zurmi

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, wanda ya bayyana cewa Turji ya rungumi shirin zaman lafiya a jihar a yayin wani taro kan tsaro a Gusau, babban birnin jihar, ya yabawa shugaban yan ta’addan kan shirinsa na barin fashin makami.

Nasiha ya bayyana cewa matakin da Turji ya dauka na kawo zaman lafiya a yankunan Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar, cewa yana kaddamar da hare-hare kan sauran ‘yan ta’adda a yankunan don tabbatar da ganin zaman lafiya ya dawo jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce:

“A yanzu Turji na kashe yan bindiga da suka ki tuba wadanda ke halaka bayin Allah a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji.”

Hedkwatar tsaro na neman manyan yan fashi 19 ruwa a jallo

Sai dai kuma, a ranar Litinin hedkwatar tsaro ta saki jerin sunayen wasu manyan yan ta’adda da kwamandoji 19 da dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro ke farautarsu.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

A cikin jerin yan ta’adda da ake nema harda Turji da Alliero wanda sarkin Yandoto, Aliyu Marafa ya nadawa sarautan Yankuzo a matsayin Sarkin Fulanin Birnin Yandoto.

Hedkwatar tsaron ta kuma sanar da kyautan naira miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanan da zasu kai ga kamun shugabannin yan ta’addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng