Sabon Tashin Hankali Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Kashe Tsohon Kwamishina, Ɗan Uwansa, Da Wasu Mutum 2

Sabon Tashin Hankali Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Kashe Tsohon Kwamishina, Ɗan Uwansa, Da Wasu Mutum 2

  • Yan bindiga sun kashe Cif Gab Onuzulike, tsohon kwamishina a jihar Enugu da dan uwansa a ranar Juma'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa daga bisani yan sanda sun bindige biyu cikin maharan sun kuma kwato motar Onuzulike
  • Hakazalika, yan bindiga sun kuma bindige wasu mutane biyu har lahira a garin Aguikpa da ke karamar hukumar Nkanu East

Jihar Enugu - Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka Cif Gab Onuzulike, tsohon kwamishina a jihar Enugu da wasu mutane uku, rahoton The Nation.

A cewar Sahara Reporters lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, a karamar hukumar Oji River da garin Aguikpa da ke karamar hukumar Nkanu East na jihar.

Taswirar Jihar Enugu
Sabon Tashin Hankali Yayin Da Ƴan Bindiga Suka Kashe Tsohon Kwamishina, Ɗan Uwansa, Da Wasu Mutum 2 a Enugu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Halaka Babban Limami Da Wasu Mutum 2 a Wata Jahar Arewa

Onuzulike wanda kuma tsohon shugaban karamar hukuma ne a Oji-River an kashe shi ne tare da dan uwansa.

A cewar rahotanni, marigayin yana dawowa ne daga wurin jana'iza kafin yan bindigan suka tare su.

Da farko yan bindigan sun tafi da tsohon kwamishinan ne kafin suka kashe shi suka dauke motarsa, sun bindige dan uwansa nan take.

Yan sanda sun bindige 2 cikin yan bindigan sun kuma kwato motar Gab Onuzulike

Wata majiya daga rundunar yan sanda ta ce yan sanda sun bindige biyu cikin maharan har lahira kuma an kwato motar marigayin daga hannun yan bindigan.

Yan bindiga sun halaka wasu mutum biyu a Aguikpa

Kafin kashe tsohon kwamishinan an rahoto cewa an bindige mutane biyu har lahira a garin Aguikpa da ke karamar hukumar Nkanu East a Enugu a ranar Juma'a.

Wadanda aka kashe din sune Ikechukwu Nnamani, tsohon shugaban unguwar Oruku da wani Ndubisi Nnamani, dan asalin garin Aguikpa.

Kara karanta wannan

Bayan fitowarsa daga Kurkuku ranar Juma’a, an kamashi ranar Asabar yana sake tafka sata

Majiyoyi daga kauyen sun ce ana kyautata zaton wasu yan bindiga da ke yi wa tsagin Oruku a rikicin da ake yi a garin ne suka labe kusa da cibiyar lafiya a Aguikpa suka a ranar Juma'a suka bindige mutanen biyu.

Ba za a iya tabbatarwa ko yan sanda sun yi kame ba game da kisan amma majiyoyi sun ce wasu mutane sun bar gidajensu a ranar Juma'a.

Yan bindigan sun dade suna adabar mutanen yankin suna kashe su tare da kona gidaje bayan gwamnatin Enugu ta kafa kwamitin shari'a don sulhu kan rikicin Oruku da Umuode.

Kwamitin ta kammala bincike ta mika wa gwamnati shawarwarinta amma kawo yanzu ba a aiwatar ba.

A kalla mutane 12 suka rasu sakamakon rikici tsakanin garuruwan buyu ciki har da tsohon basaraken Oruku, Igwe Emmanuel Mbah da wasu manya.

An gano cewa yan sanda sun dauke gawar wadanda suka mutu sun kai dajin ajiyar gawa a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

N4.8bn: An kama ma'aikatan gwamnati bisa zargin sace biliyoyi na wani aiki

'Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka Uku, Sun Sace Mutane da Dama a jihar Taraba

A wani rahoton, wasu yan bindiga sun kai hari garin Bali, hedkwatar karamar hukumar Bali a jihar Taraba, inda suka kashe mutum uku kuma suka sace wasu da dama ranar Lahadi cikin dare.

Wasu majiyoyi da yawa a Bali sun shaida wa wakilin Punch cewa yan bindigan sun farmaki jami'ai a shingen bincike da ke kusa da babban Asibitin garin, daga bisani suka hari mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164