Yan Bindiga Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 2 a Sokoto

Yan Bindiga Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 2 a Sokoto

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki al'ummar yankin Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe wani babban limami a Gangara
  • Yan bindiga sun kuma farma wasu manoma yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a kauyen Dunkawa, sun kuma kashe mutum biyu da awon gaba da wasu
  • Har ila yau masu fashi da makami sun hari motocin fashinja a titin Sabon Birni-Isa yayin da suke hanyar zuwa cin kasuwa, sun lale masu kudade da abubuwan amfani

Sokoto - Rahotanni daga Daily Trust sun nuna cewa yan bindiga sun kashe mutane uku ciki harda babban limamin Gangara a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

An tattaro cewa an kashe limamin wanda ake kira da Liman Na-Kimba a ranar Laraba yayin da yake dawowa daga Sokoto inda ya je karbar kudin fansho dinsa.

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 2 a Sokoto Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar wasu shaidu, motocinsu ya fada komadar yan bindiga a hanyar kauye Adamawa sai makasansu suka bude masu wuta.

Majiya ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Daya daga cikin harsasan ya samu limamin ya kuma kashe shi."

Yan bindiga sun halaka manoma biyu a kauyen Dunkawa

A halin da ake ciki, yan bindiga sun kuma kashe wasu manoma biyu a kauyen Dunkawa karkashin yankin Gatawa duk a karamar hukumar ta Sabon Birni kwanaki hudu da suka shige.

Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu manoma shida yayin da suke aiki a gonakinsu.

Shugaban kungiyar yan banga a Sabon Birni, Musa Muhammad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an kashe manoman ne a gonakinsu kwanaki hudu da suka shige.

Ya ce:

"Sun same su suna aiki a gonakinsu, sai suka kashe biyu sannan suka sace wasu shida."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Jama’ar Ngala da N255m, Kayan Abinci da Sutturu

A cewarsa an binne duk mamatan daidai da koyarwar addinin Musulunci. Ya koka cewa yan bindigar sun kawo dabbobi don lalata gonaki a garuruwan.

Mahara sun yiwa fasinjoji fashi a titin Sabon Birni-Isa

A wani ci gaban, yan fashi sun toshe Sabon Birni-Isa a ranar Alhamis sannan suka yiwa fasinjoji fashin kudade da sauran kayayyakinsu.

Muhammad ya fadama jaridar cewa mutanen da abun ya ritsa da su suna a hanyarsu ta zuwa kasuwar mako da ke ci a karamar hukunar Shinkafi ta jihar Zamfara daga Sabon Birni.

Ya bayyana cewa, lamarin ya afki ne a hanyar kauyikan Makwaruwa -Turba da misalin karfe 8:00am.

Ya ce yan bindigar sun shafe fiye da awa biyu suna fashi a hanyar amma babu wani rahoto na kisa ko sace wani.

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel