Dalibin Jami’ar Legas Ya Yanki Jiki Ya Fadi Matacce a Filin Kwallon Cikin Makaranta
- Wani dalibi ya kwanta dama bayan jin alamar rashin lafiya kana ya tafi buga kwallon a kafa a cikin jami’ar Legas
- An fara binciken gawa don gano ainihin abin da ya kashe wannan dalibi da ya yanki jiki ya fadi matacce
- A bangare guda, wasu ahali sun mutu baki dayansu bayan cin abincin dare, lamarin da ya tada hanakalin jama’a
Jihar Legas - An shiga tashin hankali a jami’ar Legas a ranar Lahadi yayin da wani dalibi dan aji daya mai suna Simon Adokwu ya yanki jiki ya fadi matacce yayin da yake buga wa san kwallon kafa a cikin jami'ar da ke Akoka a jihar Legas.
Punch ta ruwaito cewa, bayan da Adokwu ya halarci ibadar coci ta ranar Lahadi ya zarce zuwa filin kwallo don taka leda a wani wuri a cikin jami’ar.
An ce dalibin yana tsaka da buga kwallon ne tare da abokansa kawai aka ga ya yanki jiki ya fadi.
A kokarin ceto shi, abokansa suka garzaya dashi asbiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa nan take.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tabbatar da mutuwar Adokwu
Jami’ar hulda da jama’a ta jami’ar, Alagba Ibraheem ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, inda tace dama dalibin mai shekaru 22 ya yi korafin rashin lafiya kafin tafiya filin kwallon.
Ta kara da cewa:
“Amma a haka yace zai tafi ya buga kwallon kafa. A garin wasa, abokansa suka juyo suka ga ya yanki jiki ya fadi.
“Sun yi kokarin zuwa inda yake suka daga shi, sai suka ji baya motsi. Abokan nasa sun dauke shi zuwa asibiti, kuma sun yi kokarin ceto shi, amma abin takaici ya rasu."
Ta kuma bayyana cewa, an kira iyayen dalibin, sun kuma zo sun bayyana bukatar daukar dansu amma aka hana su, PM News ta ruwaito.
Ta kara da cewa, al’adar jami’ar ce ta yi bincike don gano musabbabin mutuwa kafin mika gawa ga dankinta.
Ya zuwa yanzu dai an dauki gawar asibitin koyarwa na LUTH da ke Idi-Araba a jihar ta Legas.
A wani labarin kuma, kunji yadda wasu ahalin mutum shida suka rasa rayukansu bayan cin abincin da ake zargin yana dauke da guba a cikinsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, ahali mai mata da miji da 'ya'ya hudu sun ci abincin dare ne kana suka kwanta, washegari aka samu duk sun mutu.
Asali: Legit.ng