Zaben 2023: Hukumar DSS Ta Ja Kunnen 'Yan Daban Siyasa A Jihar Kano

Zaben 2023: Hukumar DSS Ta Ja Kunnen 'Yan Daban Siyasa A Jihar Kano

  • Hukumar yan sandan farin kaya DSS ta jihar Kano ta gargadi yan siyasa kan cewa ba za ta lamunci daba ba gabanin, yayin da bayan zabe
  • Shugaban DSS na Kano, Alhassan Muhammad ne ya bada wannan gargadin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da INEC ta shirya
  • Muhammad ya yi gargadin cewa wasu sun fara lalata kayan kamfen a gari yana mai cewa jami'ansu za su fara farautarsu

Jihar Kano - Alhassan Mohammad, Shugaban hukumar yan sandan farin kaya DSS reshen Jihar Kano, ya gargadin cewa hukumar ba za ta amince da bangar siyasa ba gabanin babban zaben 2023.

Kamar yadda Punch ta rahoto, Direktan na DSS ya bada wannan gargadin ne ranar Alhamis a wurin taron masu ruwa da tsaki na zabe, wanda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta shirya a Kano.

Kara karanta wannan

Rikici: An tasa keyar fasto zuwa magarkama bayan cinye kudin wata malamar makaranta

taswirar jihar Kano
2023: Hukumar DSS Ta Gargadi Yan Daban Siyasa A Jihar Kano. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Duk wanda muka kama yana dabar siyasa ba za mu sassauta masa ba - Shugaban DSS na Kano

Muhammadu ya ce ba za a lamunci duk wani abu da ka iya tada rikici a jihar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ina son kira ga yan siyasa su gargadi magoya bayansu kan lalata kayayakin kamfen a birnin. Wannan shine abin da ke tashe a Kano kuma idan ba a dakatar ba, zai janyo abu mai hatsari.
"Amma kafin hakan ya faru, za mu tura jami'an mu su binciko duk masu yin hakan. Yanzu, lokaci ne na yi musu gargadi saboda ba zan saurari wani roko ba idan an kama wani.
"Don haka, duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a kotu ko shi wanene. Abin ya isa haka."

A bangarensa, shima kwamishinan yan sandan Kano ya jadada cewa za su yi duk mai yiwuwa don ganin an yi zabe lafiya kuma ba za su nuna bangaranci ba yayin zaben, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

'Na Maka Magiya Dan Allah' Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Roki Wike Ya Goya Masa Baya a 2023

Sanatan Kano Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara a 2023, Yace Ba a Maganar NNPP

A wani rahoton, Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kudancin Kano a majalisar dattawa ya ce jam’iyyar hamayya ta NNPP ba za ta kawowa APC barazana ba.

The Cable ta kawo rahoto cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a gidansa da ke garin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel