An Gurfanar Da Shugaban NURTW Saboda Lalata Allon Tallan Tinubu a Jihar Babban Jihar PDP
- An gurfanar da shugaban haramtaciyyar kungiyar NURTW na jihar Oyo, Mukaila Lamidi, wanda aka fi sani da Auxiliary a kotu kan lalata allon tallar Bola Tinubu da wasu yan takarar APC a jihar
- Shugaban kungiyar direbobin na fuskantar tuhume-tuhume 6 masu alaka da barna da gangan na yan takarar APC a Igbo-Ara a Ibadan
- Kwamishinan yan sanda na jihar ta Oyo ne ya gurfanar da shi Lamidi a madadin gwamnati
Ibadan, Oyo - An gurfanar da Mukaila Lamidi, da aka fi sani da Auxilliary, shugaban haramtaciyar kungiyar direbobi NURTW na jihar Oyo a kotu kan lalata allon kamfen din Bola Tinubu, The Nation ta rahoto.
Bola Tinubu shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 kuma jam'iyyar PDP ce ke mulki a Oyo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayannan baya-bayan nan kan Bola Tinubu, APC, Auxilliary, zaben 2023, PDP, jihar Oyo
Ana zargin Auxiliary ta lalata allon kamfen din Tinubu da na wasu yan takarar jam'iyyar APC a jihar, rahoton The Nation.
Takardar karar ta nuna cewa ana tuhumar Auxilliary da aikata laifuka 6 masu alaka da lalata allunan kamfen da gangan na yan takarar jam'iyyar APC a Igbo-Ara da Ido a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Kwamishinan yan sandan jihar ne ya gurfanar da shugaban kungiyar direbobin a madadin gwamnati.
Dalilin da yasa APC ta maka shugaban NURTW a kotu a Oyo
Jam'iyyar APC reshen jihar Oyo ta dade tana kokawa game da yan daba da ake zargin na yi wa Auxilliary aiki a jihar.
An kuma zargi magoya bayansa ga kai wa jiga-jigan jam'iyyar APC hari a lokuta daban-daban a babban birnin jihar, Ibadan.
Ana jiran zuwan shugaban kungiyar direbobin kotu a lokacin hada wannan rahoton.
Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja
A bangare guda, Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023 ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a birnin tarayya Abuja
CAN tunda farko ta nuna cewa ba ta goyon bayan tikitin musulmi na musulmi na jam'iyyar APC ta yi bayan zaben Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.
Asali: Legit.ng