Matata Bata Ganin Girma Na, Ta Zuba Mun Guba a Abinci, Miji Ya Nemi Saki a Kotu

Matata Bata Ganin Girma Na, Ta Zuba Mun Guba a Abinci, Miji Ya Nemi Saki a Kotu

  • Wani magidanci ya garzaya Kotun Kostumare a birnin tarayya Abuja ya nemi a raba aurensa da matarsa domin tana neman halaka shi
  • Mista Onu ya gaya wa Kotun cewa matar tana zargin wai zai yi asirin kuɗi da ita, ta zuba masa guba a abinci
  • Alkalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau ya ɗage zaman bayan wacce ake ƙara ta musanta tuhumar da mijin ke mata

Abuja - Wani ma'aikacin gwamnati, Mista Nnadi Onu, a ranar Laraba, ya roki Kotu ta amince ta raba aurensa da masifaffiyar matarsa, Ogechukwu, kan zargin da take masa cewa zai yi asiri da ita.

A ƙarar neman kawo ƙarshen aurensu da ya shigar a Kotun Kostumare dake zama a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, Mista Onu yace ya rasa dalilin da yasa matarsa ke masa wannan zargin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Ta'adda Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Wani Gwamna Ya Yi Murabus

Matsalolin aure.
Matata Bata Ganin Girma Na, Ta Zuba Mun Guba a Abinci, Miji Ya Nemi Saki a Kotu Hoto: vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito Magidancin na cewa:

"Bansan meyasa take zargi na da irin haka ba, hakan na nufin babu sauran yarda da juna a taskaninmu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai shigar da ƙara ya shaida wa Kotu cewa matar ta kuma yi masa barazanar kisa ta hanyar amfani da guba, "Jim kaɗan bayan tamun barazana na kama rashin lafiya kuma aka gano na ci abinci mai guba."

Bugu da ƙari ya faɗa wa Alkalin Kotun cewa matarsa bata ganin girmansa, ga rashin son zaman lafiya, a cewarsa ta kan zo har Ofis ɗinsa ta ci masa mutunci ta kama gabanta.

"Bata ganin girman kowa, 'yan uwana na jini sun daina ziyarta na. Nima kawai na tattara kayana na barta, saboda haka ne yanzun nake son a datse igiyoyin aurenmu kowa ya huta.'

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wani Babban Filin Wasanni a Najeriya Ya Ruguje, Mutane Sun Rasa Rayukansu

Sai dai a nata ɓangaren, wacce ake ƙara, Ogechukwu, ta musanta baki ɗaya korafin da mijin ya ɗora a kanta.

Wane mataki Kotun ta ɗauka?

Bayan sauraron kowane ɓangare Alkalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau, ya ɗage zaman zuwa ranar 21ga watan Nuwamba, 2022, kamar yadda NAN ta ruwaito.

A wani labarin kuma Wani Magidanci da ya nemi saki a Kotu, ya labarta wa Alkali yadda ya kama matarsa tana lalata da ɗan uwansa

Mutumin ɗan kasuwa a birnin tarayya Abuja, Justine Onu, ya gaya wa Alkali cewa matarsa na da halin kwanciya da duk wanda ta samu dama.

A cewarsa har hawan jini ta sa masa sakamakon munanan halayenta, don haka ya gaje yana rokon Kotu ta kawo ƙarshen aurensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262