Bayan Dogon Lokaci, an Gamu Tsakanin Tinubu da Kungiyar Kiristoci Ta CAN
- Da takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya shiga tattaunawa da kungiyar Kiristocin Najeriya a birnin tarayya
- CAN ta hada wani zama da 'yan takarar shugaban kasa don bayyana musu muradan mabiya addinin Kirista a Najeriya gabanin zaben 2023 mai zuwa
- Kiristocin Najeriya karkashin CAN sun sha bayyana adawa da tafiyar Bola Tinubu tun bayan da ya zabi Shettima a matsayin abokin takararsa
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya shiga tattaunawa da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Abuja.
Manufar tattaunawar dai ba komai ne face CAN ta tabbatar da cewa Tinubu ya fahimci bukatu da muradan Kiristocin Najeriya ta hanyar bayyana ka'idojin da suke so a gabatar a gwamnatinsa.
An fara taron ne tun jiya, inda aka tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AA, Manjo Hamza Al-Mustapha mai riya, rahoton Punch.
Wadanda suka halarci zaman daga bangaren Bola Ahmad Tinubu
Wadanda Tinubu ya zo dasu un hada da shugaban majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila da Sanata Orji Kalu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, Hope Uzodinma na jihar Imo, Abdulrahman Abdulrazak na jihar da gwamna Ganduje na Kano duk sun hallara.
A bangare guda, akwai ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki, Vanguard ta ruwaito.
Idan baku manta ba, Bola Tinubu ya gamu da cikas daga Kiristocin Najeriya tun bayan da ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.
Kiristocin Najeriya, ciki har da wasu shugabannin CAN sun bayyana adawarsu da tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC a matakin shugaban kasa.
Har yanzu dai ba a gama warware matsalar ba, amma ana kyautata zaton zaman Tinubu da CAN na yau zai amsa wasu tambayoyi da dama na Kiristocin kasar nan.
Tinubu ya caccaki Atiku da Peter Obi
A wani labarin, Bola Ahmad Tinubu ya caccaki 'yan takarar shugaban kasa daga jam'iyyun LP da PDP, Peter Obi da Atiku Abubakar.
Tinubu ya shaidawa duniya cewa, Atiku da Obi a kan kuskure suke, don haka dukkan manufofinsu ba masu kyau bane.
Ya bayyana wadannan maganganu ne a birnin Jos yayin kaddamar da gangamin kamfen dinsa na farko gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Asali: Legit.ng