Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Yadda Aka Hallaka Basarake a Jihar Imo

Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai da Yadda Aka Hallaka Basarake a Jihar Imo

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da harin da aka kai kan basaraken gargajiya a jihar Imo
  • Wannan na zuwa ne a makon nan bayan da rahotanni suka bayyana yadda 'yan ta'adda suka farmaki jama'a a Imo
  • Jihar Imo na daya daga jihohin da 'yan ta'adda suka addaba a 'yan shekarun nan, ana zargin 'yan IPOB da barna a yankin Kudu maso Gabas

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana kaduwa da samun labarin yadda wasu 'yan ta'adda suka yiwa basaraken gargajiya, Eze Ignitus Asor na yankin Obudi-Agwa a jihar Imo kisan gilla a makon nan.

Bayan yin Allah-wadai, Buhari ya umarci jami'an tsaro da su gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da tabbatar da doka a kansu.

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun tona moboyar su Turji yayin da sojoji ke neman 'yan ta'adda ruwa a jallo

Idan baku manta ba, rahoto ya bayyana yadda wasu 'yan ta'adda suka hallaka basaraken a jihar Imo.

Buhari ya yi Allah wadai da kashe basaraken Imo
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da yadda aka hallaka basarake a jihar Imo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan gillan da aka yiwa Eze Ignitus Asor, basaraken gargajiyan Obudi-Agwa a karamar hukumar Oguta ta jihar Imo da dai sauransu."

Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu

Yayin da yake mika ta'aziyya ga iyalai da 'yan yankin Obudi-Agwa, Buhari ya kuma yiwa wadanda suka raunuka a harin fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Hakazalika, ya yaba da kokarin gwamnan jihar Imo wajen haka fannin tsaro tare da karfafawa mazauna jihar gwiwar ci gaba da ba gwamnati hadin kai wajen zakulowa tare da gurfanar da masu aikata laifuka.

Yankin Kudu maso Gabas na daya daga yankunan da ake fama da hare-haren 'yan ta'adda a 'yan shekarun nan, ana zargin 'yan IPOB da tada zaune tsaye a yankin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Mai Miliyan

A wani labarin kuma kun ji cewa, mazauna jihar Zamfara sun bayyana cewa, wuraren da za a samu 'yan ta'adda a fadin kasar nan ba boyayye bane duba da yadda ake ganinsu.

Sun bayyana hakan ne a martaninsu ga rahoton sojoji na ayyana neman su Bello Turji ruwa a jallo.

'Yan Najeriya na cikin damuwar yadda 'yan bindiga keaddabarsu a shekarun nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.