Magidanci Yana Sharbar Kuka a Bidiyo Bayan Caca ta Lamushe Kudin Makarantar ‘Ya’yansa

Magidanci Yana Sharbar Kuka a Bidiyo Bayan Caca ta Lamushe Kudin Makarantar ‘Ya’yansa

  • Wani bidiyo dake yawo a soshiyal midiya, an ga wani mutum wanda yayi amfani da kudin makarantar ‘ya’yansa yayi caca ya shiga wani hali
  • A bidiyon da aka fitar a Instagram a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, an ga mutumin yana duba wasu takardu da aka gano na asusun bankinsa ne
  • A take ya rushe da kuka bayan ya gano halin da asusun bankinsa ya shiga sakamakon cacar da ya shiga ko zai yi sa’a

Martani daban-daban sun cika bayan bayyanar wani bidiyon ‘dan Najeriya da ya zabga caca da kudin makarantar ‘ya’yansa.

Magidanci Yana kuka
Magidanci Yana Sharbar Kuka a Bidiyo Bayan Caca ta Lamushe Kudin Makarantar ‘Ya’yansa. Hoto daga @thatblackbwoyy
Asali: Instagram

Kamar yadda bidiyon da aka samo daga Instagram ya nuna, mutumin ya gane barnar da ya tafka ne bayan ya samu takardun asusun bankinsa.

A bidiyon da @thatblackbwoyy ya saki a ranar Lahadi, 4 ga watan Nuwamba, mutumin cike da kunar rai ya dinga duba takardun asusun bankinsa sannan ya share hawayen da ya fito daga idanunsa.

An bayyana a bidiyon cewa, magidancin ya saba caca kuma ana kiransa da Sarkin caca na yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba a tabbatar da wannan ikirarin ba, amma magidancin ya zauna dirshan a kasa cike da damuwa.

Wasu ma’abota amfani da Instagram sun dinga tantamar cewa takardar dake hannunsa ta bankinsa ce.

Kalla bidiyon a kasa:

Martanin jama’a daga Instagram

@dj_op.cue yace:

“Ka bar caca.”

@otunba_richie7 yace:

“Rayuwa tayi zafi.”

@legend_saintwalker yace:

“Caca ta mutane ce dake son hanya mafi sauki ta azurcewa amma kuma baya yuwuwa saboda koda yaushe gidan ke ci.”

@son_of_god1930 yace:

“Wannan zai yi amfani da rayuwarsa ya cutar da ta ‘ya’yansa.”

@teezzy_12 yayi martani da:

“Caca tana zuwa da kalubale mai tarin yawa.”

@leo.cerberus yace:

“Babu sauki da.”

Wasu kan yi sa’a a caca

Wasu mutanen kan shiga caca sannan su samu sa’a yayin da wasu ke shiga da kafar hagu inda suke tafka mutuwarta asara.

A wani labari na daban, wani saurayi ya dauka dubu goma daga dakin budurwarsa inda yaje ya shiga caca sannan yayi nasarar samun miliyoyi.

Wannan ya kawo tarzoma Tsakanin da da Budurwa wacce ta dire gefe bayan ya bata kyautar dubu hamsin a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel