Ma'aikatu Sun Kashe N2tr a Boye ba Tare da Sanin Shugaban kasa da 'Yan Majalisa ba
- Ana zargin wasu ma’aikatun tarayya sun batar da N2tr ba tare da sanin ‘Yan majalisan Najeriya ba
- ‘Yan majalisar sun aika goron gayyata ga hukumomi 63 da ake zargin sun sabawa dokar batar da kudi
- Bayan wani bincike, Majalisar wakilai tace a soke ma’aikatun NEMSA da NDE da ke aiki a kasar nan
Abuja - Kwamiti na musamman da aka kafa domin binciken ayyukan ma’ikatun gwamnatin tarayya ya bada shawarar rusa wasu hukumomin kasar.
Vanguard tace wannan kwamiti yana ganin akwai bukatar a soke hukumar NDE mai samar da ayyukan yi da hukumar kula da lantarki na kasa, NEMSA.
A zaman da aka yi, ‘yan kwamitin majalisar wakilan tarayya sun ce wadannan hukumomi ba su iya sauke nauyinsu ba, amma ana ta kashe masu kudi.
Kwamitin ya bukaci hukumar NDE ta gabatar da abubuwan da ta tabuka na tsawon shekaru biyar. A karshe aka gamsu cewa ba a bukatar aikin da suke yi.
NELMC da NAPTI sun sha
Shugaban kwamitin, Hon. Victor Mela Danzaria yace sun zauna da hukumomin NELMC da NAPTI, amma su ba su cikin wadanda aka nemi a ruguza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Adedeji Olajide wanda yana cikin kwamitin, yace NEMSA ba ta da amfani, don haka bai dace gwamnati ta cigaba da kashe mata kudi duk shekara ba.
Ba a gamsu da aikin NEMSA da NDE ba
Shugaban NEMSA na kasa, Injiniya Aliyu Tukur yace an kafa su ne a 2015 domin a rika samun lantarki ta hanyar tabbatar da cewa an tanadi kayan aiki.
Abubakar Nuhu wanda shi ne shugaban NDE yace aikinsu shi ne samar da ayyukan yi a fadin kasar nan, amma majalisa tace hukumar ba ta yin aikinta.
An yi bindiga da N2tr
A wani rahoton daga jaridar, kwamitin PACAC a majalisar wakilan tarayya ya gayyaci hukumomin gwamnatin tarayya 63 domin yi masu tambayoyi.
Kwamitin yace binciken da suka yi ya nuna hukumomi da ma’aikatun gwamnatin sun saba doka ta hanyar kashe N2tr ba tare da amincewar majalisa ba.
Shugaban kwamitin, Hon. Oluwole Oke yace sun aika takarda zuwa ga Shugaban ofishin kasafin kudi domin kawo masu takardun kasafin da suka amince da shi.
Hon. Oke yake cewa shugaban kasa bai gabatar da kasafin kudinsu ba, amma ma’aikatun nan sun kashe kudin da ‘yan majalisa ba su san da zamansa ba.
Jirgin kasan Abuja zai dawo aiki?
An samu labari cewa Shugaban Hukumar NRC da ke kula da harkokin jirgin kasa, Fidet Okhiria, ya yi fatali da rade-radin da ake yadawa na dawowa aiki.
Rabon da jirgin kasan Kaduna-Abuja ya dauki fasinjoji tun watan Maris, Fidet Okhiria yace ana kokarin komawa aiki kafin karshen watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng