Fetur Zai Iya Haura N400, Gwamnoni Sun Bada Shawarar Gaggauta Janye Tallafi
- Gwamnonin Najeriya da masu ruwa da tsaki sun halarci taron NESG na 28 da ake yi a garin Abuja
- A wajen taron, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnati tayi watsi da tsarin tallafin fetur
- Gwamnoni sun ce akwai rashin gaskiya a tsarin, kuma kokarin rage farashin mai ya durkusa kasa
Abuja - Mai girma Gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bada shawarar a gaggauta cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya take biya.
Vanguard tace Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen taron NESG da ake yi a garin Abuja.
Da aka tambayi gwamnan na jihar Kaduna a kan abin da ya kamata gwamnatin tarayya tayi, sai yace a gaggauta watsi da tsarin tallafin man fetur.
Gwamnan yace gwamnonin jihohin kasar nan 36, jami’an gwamnatin tarayya da majalisar tattalin arziki sun amince a cire tallafin tun Satumban 2021.
An yi watsi da maganar da aka yi
Nasir El-Rufai yake cewa ya yi mamaki da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ki dabbaka wannan matsaya duk da matsalar da biyan tallafin ya jawo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Gwamnan, daukar nauyin farashin fetur da gwamnatin Najeriya take yi, ya jefa kasar a cikin kalubale, baya ga rashin gaskiya da ake tafkawa.
A rahoton Leadership, an ji El-Rufai da takwarorinsa na Edo da Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya da Gwamna Godwin Obaseki sun yi wannan kira.
...ana bukatar wutar lantarki
Gwamnonin jihohin sun ce ya kamata gwamnatin tarayya tayi maza-maza ta dakatar da tsarin biyan tallafin fetur, kuma a inganta wutar lantarki.
A wannan taro wanda shi ne na 28 a tarihi, gwamnonin sun nemi gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci da ta sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya.
Yayin da El-Rufai ya dage kan harkar man fetur, rahoton yace Mai girma Obaseki ya nuna damuwarsa a kan sha’anin lantarki domin a samu ayyukan yi.
Shi kuma Gwamna Inuwa na jihar Gombe yace ya kamata a canza fasalin kasa ta yadda kowace jiha za ta amfana da bangaren da tayi fice kan ‘yar uwarta.
Za a biya tallafin fetur a 2023?
A baya kun ji labari shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudi a kan tallafin man fetur duk shekara.
Shugaban kasar yake cewa gwamnatinsa ta batar da N1.5tr a cikin watannin shidan farkon 2022. Wannan ne ya sa aka cire tallafin daga kasafin kudin badi.
Asali: Legit.ng