Mawaki Portable Ya Fusata Yayin da Ya Gano Masoyansa Sun Watsa Masa Kudaden Bogi

Mawaki Portable Ya Fusata Yayin da Ya Gano Masoyansa Sun Watsa Masa Kudaden Bogi

  • Fitaccen mawakin nan na Najeriya, Portable ya bayyana a kafar sada zumunta domin caccakar wasu 'yan Najeriya da suka watsa masa kudin bogi a kulob
  • Mawakin wanda ya bayyana zuwa birnin Fatakwal domin yin wasa a gidan kulob ya nuna bacin ransa ga abin da ya faru
  • A bidiyon da Portable ya yada, ya nuna kudaden da aka watsa masa a kulob din, lamarin da ya dauki hankalin jama'a

Fitaccen mawaki a Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya sanya jama'a cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ya bayyana yadda wasu masoyansa suka watsa masa kasa a ido.

Mawakin ya fito ya bayyana cewa, wasu mutane a kulob sun yi masa yayyafin kudaden bogi yayin da yake tsaka da rawa da waka.

A wani bidiyon da ya yada a shafinsa, an ga mawakin na yaga wasu kudaden da yace na bogi ne tare da yiwa wadanda suka ba shi su tofin Allah-tsine.

Mawaki ya fusata yayin da aka watsa masa kudin bogi
Mawaki Portable Ya Fusata Yayin da Ya Gano Masoyansa Sun Watsa Masa Kudaden Bogi | Hoto: @portablebaeby
Asali: Instagram

Hakazalika, Portable ya ci gaba da caccakar masoyansa 'yan birnin Fatakwal saboda yadda suka bari aka ci masa fuska.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ji shi yana cewa, jama'ar Fatakwal basu nuna masa kauna ba.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@richie.richie127:

"Lallai fa, kudaden bogi."

@hon_armani25:

"Na tabbata yayin da kake ganinsu da damin 'yan 1k, ka kara kaimin rawa da waka, yi hakuri baba oloye."

@imindz_orf:

"Ka watsa na gaske sun watsa maka na bogi."

@topboi_rd:

"Mutumin ya yi sa bai gane na bogi bane tun a kan dandamali, Portable da ya gama dashi cikin gaggawa."

@official_kiski:

"Mama zeh na kirga kudaden bogi."

@cherry__x01:

"Sun cuce ka!! Ka watsa kudin gaske sun watsa maka na bogi ya kamata ka koyi darasi daga Fatakwal."

@aremo_hibee_dende:

"Ka watsa kudin gaske da yamma, yaran Fatakwal sun watsa maka na bogi da dare."

Ango ya hana a kira shi bayan 7 na dare jim kadan bayan shiga daga ciki

Wani ango kuma da ya samu wuri ya baje kolin halinsa, inda yace sam bai amince abokansa su sake kiransa ba bayan karfe 7 na dare.

Ya bayyana hakan ne a gaban kowa, inda ya gargadi jama'a da cewa su kula cikin raha.

Jama'ar da suka halarci auren sun yi dariya tare da taya shi murnar gama gauranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel