Zargin Boye Biliyoyi Nairori a Abuja: Matawalle Ya Rubuta Wasika Ga EFCC
- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce zai ba hukumar EFCC damar binciken gidansa wanda ake zargin an gano makudan kudade boye a cikinsa
- Matawalle ya ce labarin da ke yawo cewa an gano biliyoyin nairori a gidansa da ke Abuja ba komai bane face karya da yunkurin bata masa suna
- Ya ce ya kadu matuka a lokacin da ya yi karo da labarin wata jaridar yanar gizo cewa an gano kudade boye a gidansa da na Ganduje da Wike
Abuja - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rubuta wasikar korafi ga hukumar EFCC kan zargin da ake masa na boye biliyoyin kudade a gidansa da ke Abuja.
Matawalle ya bayyana zargin a matsayin kanzon kurege mara tushe balle makama, jaridar Leadership ta rahoto.
A cikin wata wasika dauke da sa hannun lauyansa Cif Mike Ozekhome (SAN), gwamnan ya nanata cewa zargin baida tushe, karya ne kuma baida makama" domin an bude gidan ne ta karfin tuwo kuma ba a samu wani abu mai kama da haka ba.
Matawalle ya ce wallafar da wata jaridar yanar gizo tayi ba komai bane face yunkurin bata masa suna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Ya kadu matuka da aka janyo hankalinsa zuwa ga wani labari da Sahara Reporters ta wallafa mai taken: "An ga biliyoyin naira da aka boye a Abuja, Kano da Port Harcourt, a gidajen Wike, Ganduje da Matawalle."
Ozekhome ya ce kanen labarin na karya ya bata sunan gwamnan tare da kawo masa tozarci.
Matawalle ya ce a shirye yake ya ba damar gudanar da cikakken bincike kan zargin domin gano gaskiya lamari.
Matawalle bai taba biyan albashi da tsabar kudi ba - Dosara
Hakazalika, kakakin gwamnan na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara, ya bayyana cewa Matawalle bait aba biyan ma’aikata albashi da tsabar kudi ba kuma ba zai taba yin hakan ba a daidai wannan lokaci da gwamnati ta yarda da aiwatar da biyan karancin albashi na 30,000 ba.
Dosara ya ce Matawalle ya jajirce ne wajen kula da jin dadi da tsaron rayuka da dukiyoyin mutanen jihar kuma ba zai bari makiyan jihar sun janye masa hankali daga kyakkyawan aikin da yake yi ba, Channels TV ta rahoto.
EFCC bata sanya idanu kan Ganduje ba
A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin Kano ta fito ta karyata rahotannin da ke yawo cewa gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje na daga cikin wasu gwamnoni da EFCC ke lura da motsinsu saboda zargin su da boye kudade a gidajensu.
Gwamnatin ta ce asali ma hukumar EFCC bata ambaci sunan kowa ba amma sai wata jaridar yanar gizo ta yi gamon kanta wajen wallafa sunan ganduje cikin gwamnoni uku da tace ana zargi.
kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce sam labarin bai da asali duk yunkuri ne na bata sunan gwamnan.
Asali: Legit.ng