Sauya Naira: Ganduje Baya Cikin Wadanda EFCC Ta Zuba Idanu A Kansu, Gwamnatin Kano

Sauya Naira: Ganduje Baya Cikin Wadanda EFCC Ta Zuba Idanu A Kansu, Gwamnatin Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi wani rahoto da ke ikirarin cewa Gwamna Ganduje na cikin jerin gwamnoni uku da EFCC ke sanyawa ido saboda boye kudade a gidajensu
  • Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce rahoton wani yunkuri ne na bata sunan gwamnan
  • Garba wanda ya nemi a janye labarin yace Gwamna Ganduje bai mallaki biliyoyin nairori ba balle kuma ya boye su

Kano – Gwamnatin jihar Kano ta karyata rahotannin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na cikin jerin gwamnoni uku da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta zuba idanu a kansu kan cewa sun boye kudade a gidajensu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnati ta yi martani ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya fitar a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

Ganduje
Sauya Naira: Ganduje Baya Cikin Wadanda EFCC Ta Zuba Idanu A Kansu, Gwamnatin Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Kwamishinan ya bayyana cewa yayin da EFCC bata ambaci sunayen gwamnonin ba, jaridar yanar gizon ta yi gaban kanta wajen yin wannan kagen.

Ya ce mawallafin rahoton wanda baida tushe balle makama hasashe yana hasashe ne kawai ko kuma dai an kagi labarin ne don bata sunan gwamnan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Garba ya bayyana cewa Gwamna Ganduje bai mallaki biliyoyin nairori sannan ya yi ruf da ciki a kansu ba.

Kwamishinan ya kara da cewa Kano na daya daga cikin yan tsirarun jihohi da ke biyan albashin ma’aikatanta a kan kari, yana mai cewa a daidai lokacin da aka saki rahoton karyan, an rigada an fara tura albashin watan Oktoba.

Don haka, yay i kira ga janye labarin sannan mawallafansa sun bayar da hakuri, kuma cewa rashin aikata hakan zai sa gwamnatin jihar ta dauki mataki na doka, rahoton Ripples Nigeria.

Kara karanta wannan

Buhari Na Shirin Kashe Biliyan 2 Domin Sabunta Motocin Aso Villa

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

A baya, mun ji cewa an sanyawa gwamnoni uku dake kan karagar mulki ido kan yadda zasu yi da makuden biliyoyin da suka boye kuma suke don biyan albashin ma’aikata da su, shugaban Hukumar yaki da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya sanar da Daily Trust a zantawar da suka yi ta musamman a ranar Alhamis.

Yace samamen da suke kaiwa ‘yan canji zasu cigaba inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayansu domin amfanin kowa.

aily Trust ta rahoto cewa, babban bankin Najeriya a ranar 26 ga watan Oktoban 2022 ya sanar da cewa kasar nan zata canza wasu takardun kudadenta domin dakile matsalolin tattalin arziki da suka addabeta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel