2023: Ɗalibai Mata Musulmi Na Najeriya Sun Bayyana Ƴan Takarar Da Za Su Zaɓa

2023: Ɗalibai Mata Musulmi Na Najeriya Sun Bayyana Ƴan Takarar Da Za Su Zaɓa

  • Bangaren mata na kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya, MSSN, reshen jihar Legas ta ce yan takara da za su mutunta damar saka hijabi kawai za su zaba
  • Shugaban kungiyar ta reshen jihar Legas, Basheeroh Majekodunmi, ne ta bayyana hakan a wurin wani taro da mataimakiyarta Azeezah Gidigbi ta wakilce ta
  • MSSN ta ce tana bukatar shugabanni da za su jadada dokar da za ta bawa mata saka hijabi a makarantu, wurin aiki da cikin gari ba tare da tsangwama ba da kuma rikon amana da gaskiya da tsari mai kyau

Legas - Reshen mata na kungiyar musulmi na Najeriya, reshen jihar Legas ta bukaci mambobinta da wasu mata musulmi a kasar su zabi wadanda za su mutunta damarsu na saka hijabi a makarantu da wuraren aiki, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ASUU ta magantu kan za ta fara sabon yajin aiki ko kuma za ta ci gaba da aiki

Ta bukaci su yi la'akari da abubuwan da yan takarar suka yi, da biyayya ga kundin tsarin da kotu, halayarsu, halayen jagoranci da yiwuwar kawo canji a Najeriya.

MSSN Logo
2023: Dalibai Mata Musulmi Na Najeriya Sun Bayyana Yan Takarar Da Za Su Zaba. Hoto: The Nation News
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta bada wannan sharrudan ne yayin taron wayar da kai na shekarar 2022 da Lagos Sisters Circle ta shirya inda ta bukaci mata su shiga siyasa a dama da su.

Dalibai musulmi sun bada sharadin goyon baya

Mataimakiyar Amirah na MSSN Legas, Azeezah Gidigbi, wanda ta gabatar da jawabin maraba a madadin Amira na Legas, Basheeroh Majekodunmi, ta ce ya zama dole yan Najeriya su zabi shugabanni da za su tabbatar da tsaron dalibai musulmi a makarantun sakandare da dukkan matakai.

Ta ce:

"Muna bukatar gwamnati da za ta tabbatar za mu iya saka hijabi a makarantu, wurin ayyuka da gari ba tare da tsangwama ba. Yana da kyau mu wayar da kan iyayenmu kan zaben shugabanni masu nagarta kuma a matsayinmu na matasa su shiga harkokin zabe."

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

A jawabinta, shugaban kungiyar kare hakkin saka hijabi, Mutiat Orulu-Balogun, ta ce mata su karfafawa sauran mata gwiwa su yi zabe, Daily Trust ta rahoto.

Ta kara da cewa:

"Mu sanar da yan siyasa matsalolin da ke fuskantar mu kuma mu tabbatar sun cika alkawuran da suka yi."

Damar saka hijabi na da muhimmanci

A bangarenta, tsohuwar Amirah na MSSN Legas, Hafsah Badru, ta jadada cewa mutunta yancin sanya hijabi ba alfarma bane.

Ta ce:

"Za mu yi la'akari ne kawai da dan takarar da zai mutunta doka da hukuncin kotu, ciki har da bayyana goyon baya da kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan amfani da hijabi. Wannan ba lamari ne na kashin kai ba amma wani abu ne da Kundin Tsarin Mulki ya goyi bayansa. Bayan haka, za mu fara duba tarihin, riko da gaskiya, da tsare-tsaren yan takara."

Zaben 2023: Wasu Yan APC Suna Guna-Guni Kan Rashin Saka Sunan Tallen, Binani Da Wasu A Kungiyar Kamfen Na Mata

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Wata kungiyar goyon baya ta jam'iyyar APC mai mulki a kasa, (APCSG), ta yi korafi kan rashin saka sunan ministan harkokin mata, Pauline Tallen, Shugaban mata na kasa na APC, Dr Betta Edu, da yar takarar gwamna tilo a jam'iyyar, Sanata Aishatu Binani a kwamitin yakin zabe na mata na jam'iyyar.

Kungiyar, cikin sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 1 ga watan Oktoba mai dauke da sa hannun Dingyadi Haruna ta ce hakan na nuna alamun jam'iyyar ta na dagewa ganin ta janyo rikicin cikin gida gabanin babban zaben na 2023, Legit.ng ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164