Sauye-Sauyen NNPC: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Kyari Ya Yi Magana Kan Barazanar Kashe Shi
- Shugaban NNPP, Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewa ana barazana ga rayuwarsa saboda ayyukan sauye-sauye da ya ke yi a bangaren mai
- Kyari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya ke yin jawabi wurin taron tabbatar da gaskiya da rikon amana da majalisar wakilai ta rubuta
- A bangare guda, satar mai na karuwa a Nigeria, hakan na janyo raguwar kudin shiga duk da karuwar farashin man fetur a kasuwancin duniya amma Kyari ya ce sun rufe matattun mai wadanda ba bisa ka'ida aka bude ba
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin man Nigeria, Mr Mele Kolo Kyari, ya ce yana ta samun barazanar kisa sakamakon canje-canje da ake yi a NNPC, The Cable ta rahoto.
Kyari ya fadi hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya a wajen taron tabbatar da gaskiya da rikon amana da kwamitin majalisar dokokin tarayya kan yaki da rashawa ta shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi wa taron take da: ‘Habaka gaskiya da rikon amana a fannin mai da iskar gas: kalubale da alfano.'
Mele Kyari ya yi ikirarin rayuwarsa na ciki hatsari
Shugaban na NNPC ya ce sakamakon aiwatar da dokar bangaren man fetur na PIA, ana canje-canje da suka taba tsaffin wadanda ke morar abubuwa a bangaren, rahoton Daily Trust.
Ya bayyana cewa kamfanin ta rufe matatun mai wadanda ba bisa ka'ida ba da dama da ke shafar yawan man fetur da ake samarwa a kasar.
Kyari ya bayyana cewa sakamakon haramtattun matatun mai, man fetur da ake samarwa a kasar ya koma ganga guda dari bakwai wato 700,000.
Ya ce:
"Ina so in ce cewa wannan masana'antar na kan bakin wata canji, akwai wata babbar canji da ke faruwa da kuma yana da tsada sosai ga mutane har da ni kaina.
"Akwai barazana ga rayuwata, zan iya fadan hakan, an yi barazana ga rayuwata sai da dama amma bamu damu da wannan ba, munyi imanin babu wanda zai mutu sai lokacinsa ya yi.
"Amma wannan ne farashin sauyi. Lokacin da mutane suka bar abin da suka saba da shi kuma suka fuskanci wani sabon abu da zai rage musu daraja da kuma samu da suke da shi, za su dauki mataki. Hakan na da amfani ga dukkanmu kuma za mu yi aiki tare don tabbatar da cewa".
NNPC: Mun Gano Hanyar da Barayi Suka Yi Shekaru 9 Suna Satar Mai Ba a Ankara ba
A wani rahoton, kamfanin man Najeriya wato NNPC ya ce ya gano wata barauniyar hanya da aka yi shekaru kimanin tara ana satar danyen man kasar.
Shugaban kamfanin NNPC Limited, Mele Kolo Kyari ya yi wannan bayani ranar Talata yayin da ya je gaban ‘yan majalisar tarayya, rahoton The Cable
Mele Kolo Kyari ya shaida wa kwamitin harkar mai da gas na majalisar dattawa da na wakilai cewa a kokarin da suke yi an gano barawon bututu.
Asali: Legit.ng