Kano: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka 10, Sun Lalata Musu Amfanin Gonaki
- Kauyuka kusan goma dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano ne aka tarwatsa tare da lalata musu amfanin gonakinsu sakamakon kutsen ‘yan bindiga
- Mazauna kauyukan sun sanar da yadda rana tsaka ‘yan bindigan suka saki shanunsu cikin gonakinsu kuma suka lamushe musu amfanin gonakinsu
- Jama’ar yankin sun bayyana cewa hakan ya saba faruwa da su a shekarun da suka gabata, amma wannan karon sun mike don yin fito na fito da maharan
Kano - Kusan kauyuka 10 dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano ne aka tarwatsa tare da lalata gonakinsu.
Ganau sun ce lamarin ya fara ne yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka saki dabbobinsu inda suka cinye amfanin gonakin jama’a da ba a girbe ba.
Wani ganau yace yayin da mazauna yankin suka tunkaresu, sun yanke hukuncin kai farmaki kan mazauna kauyen tare da halaka mutum biyu.
Sunayen kauyukan da aka kai hari
Daily Trust ta rahoto cewa, wasu daga cikin kauyukan da aka kaiwa hari sun hada da Daurawa, Kuka, Bakwai, Geza, Macinawa da Kasakore.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yayin bayar da labarin yadda lamarin ya faru, wani ‘dan uwan daya daga cikin wadanda aka halaka mai suna Idi Lawan, yace an sokawa ‘dan uwansa Sanusi Usman wuka.
“Ya je gonarsa kuma ya tarar dabbobi sun cinye waken, lokacin da ya tunkaresu domin korafi, sun soka masa mashi kuma ya mutu.”
- Liman yace.
Wani mutum da ya tsallake rijiya da baya, ya matukar jigata inda ya arce da raunika, yace sun same shi har gonarsa.
“A yayin da na ga dabbobinsu suna cin gyada ta, na bukaci su bar wurin. Daga nan ban san me ya sake faruwa ba kawai suka fara sukata, ku kalla jikina.”
- Yace.
Ba mu barci da idanu rufe - Ganau
Wani mazaunin daya daga cikin yankunan da aka kaiwa farmaki, Basiru Daura Kunya, ya sanar da Daily Trust cewa maharan sun addabi yankin tun shekarar da ta gabata kuma jama’a sun gaji wanda hakan yasa suka yanke hukuncin daukar mataki wanda hakan ya kawo arangamarsu a ranar Talata.
“Jama’a basu barci a wadannan kauyukan na tsawon lokaci saboda tsoron hari kan gonakinsu da rayukansu. Wannan lamarin ne ya faru shekarar da ta gabata, muka kalmashe hannaye muka zuba musu ido.
“Gwamnati ta shigo lamarin nan ta cece mu kafin wannan abun yayi kamari.”
- Yace.
Mazauna yankunan sun tare titunan dake kaiwa Babura a jihar Jigawa a ranar Laraba domin zanga-zanga kan wannan lamarin.
’Yan sanda sun magantu
Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace:
“Tuni zaman lumana ya dawo yankin. Mutum daya ne ya rasa ransa yayin da wani ke asibiti.
“Yayin da ake cigaba da bincike kan lamarin, mun saka Miyetti Allah da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin.”
Asali: Legit.ng