‘Yan Bindigan da Suka yi Garkuwa da Yara 20 Suna Neman N40m ta Fansa
- ‘Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace yara kanana 20 inda suka nemi N40 miliyan na kudin fansa
- An gane cewa sun kwashe yaran da suka hada da mata 16 sai yara maza hudu tun kwanakin baya a yankin Kusherki dake karamar hukumar Rafi
- Mazauna yankin da iyayen yaran suna neman daukin hukumomi sakamakon labarin azabtar da yaran da aka gano ‘yan bindigan suna yi
Niger - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yara 20 masu shekaru daga hudu zuwa goma a yankin Kusherki dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Kananan yaran da aka yi garkuwa dasu sun hada da yara maza hudu da yara mata goma sha shida.
Yara sun kusa wata daya hannun miyagu
Mazauna yankin sun ce a halin yanzu yaran sun kwashe kwanaki 21 a hannun masu garkuwa da mutanen kuma suna bukatar kudin fansa har Naira miliyan arba’in.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani mazaunin yankin ya sanar da Daily Trust cewa, wadanda suka yi garkuwa da yaran sun matukar azabtar dasu yayin da suke hannunsu.
Yace iyayen yaran sun fada mawuyacin hali tun bayan da aka yi garkuwa dasu kuma sun yi kira ga hukumomi dasu taimaka musu wurin ceto yaran, jaridar Punch ta rahoto.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindiga a cikin makonnin da suka gabata sun cigaba da kai hari yankunan Magama tare da babban titin Zungeru zuwa Tegina inda suke saka tsananin tsoro a zukatan manoman dake girbe amfanin gonarsu a yanzu.
Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Ibrahim ya sanar da Daily Trust cewa da yawa daga cikin ‘yan uwansa da aka yi garkuwa dasu a watanni hudu da suka gabata suna hannun masu garkuwa da mutanen.
’Yan ta’adda sun saba kwashe yara
Ba wanna bane karo na farko da ‘yan ta’adda ke kwashe kananan yara tare da bukatar kudin fansa ba.
’Yan bindigan sun saba sace yaran makaranta inda a kwanakin baya suka kwashe ‘yan Islamiyyar Tegina dake jihar Niger.
Da kyar da makyarkyata aka samu aka ceto yaran bayan watannin da suka kwashe hannun masu garkuwa dasu.
A karshen shekarar 2020 ne ‘yan ta’addan suka gane fara kai farmaki makarantun Boko inda suka fara da kwashe yaran makarantar Kankara.
Asali: Legit.ng