Gwamnatin Buhari Ta Aikawa Gwamnoni Wasika, Ana Shirin Sakin ‘Yan Kurkuku

Gwamnatin Buhari Ta Aikawa Gwamnoni Wasika, Ana Shirin Sakin ‘Yan Kurkuku

  • Ministan harkokin gida na Najeriya ya rubuta takarda zuwa ga NGF, yana neman su yi zama na musamman
  • Rauf Ogbeni Aregbesola ya bukaci ya hadu da Gwamnonin ne kan maganar sakin wadanda su ke kurkuku
  • Wani Hadimin Aregbesola yace Ministan bai ga dalilin cigaba da tsare dubban mutane a gidan maza ba

Abuja - Rauf Ogbeni Aregbesola wanda shi ne Ministan harkokin gida, ya rubutawa gwamnoni bukatar rage adadin masu zama a gidan gyaran hali.

Punch tace Ministan harkokin cikin gidan na Najeriya ya aika takarda zuwa ga kungiyar gwamnoni kan batun rage yawan wadanda su ke tsare.

Hadimin Ministan, Sola Fasure ya fadawa ‘yan jarida Rauf Aregbesola ya nemi ya zauna da gwamnoni domin ganin yadda za a bullowa lamarin.

An daure mutane babu dalili

Kwanakin baya aka ji Ministan tarayyan yana cewa 70% na wadanda suke daure a gidan gyaran hali su na jiran Alkali ya yanke masa hukunci ne.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

Rahoton da aka fitar a yau yace a dalilin haka gwamnatin tarayya take so a fito da 30% na wadannan mutane da sun haura 75,000, su bar gidajen yari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fiye da 90% su na garkame a gidajen gyaran halin da ke kasar nan sun shiga hannu ne saboda aikata abubuwan da suka sabawa dokokin jihohin da suke.

Aregbesola
Rauf Aregbesola a ofishinsa Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Sola Fasure yace ganin halin da ake ciki ne, Aregbesola yake so a fito da wasu da aka daure, yace babu dalilin da za a cigaba da rufe su a gidajen maza.

A halin yanzu akwai kurkuku 253 a fadin kasar nan, Ministan harkokin gida yana da ra’yin cewa zai fi kyau a rage adadin fursunoni domin sun yi yawa.

"Minista ya rubuta takarda ga kungiyar gwamnonin Jihohi, amma bai zauna da su ba, saboda sai sun tuntube shi, sun sa masa lokaci tukuna.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Ya aika masu da bukata cewa yana so ya zauna da su, amma har zuwa yanzu ba su ce masa komai ba, a takaice dai ba ayi zaman nan ba.”

- Sola Fasure

Yayin da Ministan shari’a, Abubakar Malami ya je gaban Sanatoci, shi kuma ya shaida masu a shekaru shida, an saki mutane 6000 daga gidajen kaso.

An daure Liu Guoqiang

An samu labari cewa Liu Guoqiang ya gamu da hukuncin kisa a kasar Sin saboda ya karbi cin hancin Dala miliyan 48 tsakanin shekarun 2006 da 2016.

Kotu tace Mista Guoqiang ya amsa laifinsa da kan sa, sannan ya yi nadama, har an dawo da duka dukiyoyin haram da ya karba, amma zai tafi kurkuku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel