Zaɓen 2023: IGP Ya Ba Wa Ƴan Sanda Rigunan Kariya Daga Harsashi Da Kwalkwali

Zaɓen 2023: IGP Ya Ba Wa Ƴan Sanda Rigunan Kariya Daga Harsashi Da Kwalkwali

  • Za a samarwa jami'an yan sandan Najeriya rigunan kariya daga harsashi, kwalkwali da wasu kayayyakin yaki da tarzoma gabanin zaben 2023
  • Usman Baba, sufeta janar ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsaron yan Najeriya da yan sandan gabanin babban zaben
  • IGP din ya kuma yi kira ga jami'an rundunar su kasance masu da'a, biyayya ga doka da mutunta hakkokin mutane yayin gudanar da ayyukansu

FCT, Abujba - Gabanin babban zaben shekarar 2023, Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Baba, a ranar Litinin ya bada umurnin a raba wa jami'ai kayan yaki da tarzoma a sassan kasar nan.

Shugaban yan sandan ya ce kayayyakin sun hada da riga masu hana harsashi ratsa jiki, kwalkwali (hular kwano) da barkonon tsohuwa da bindiga mai kashe gabban jiki, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

IGP Usman Baba
Zaben 2023: IGP Ya Ba Wa 'Yan Sanda Rigunan Kariya Daga Harsashi Da Kwalkwali. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

An samarwa yan sandan kayayyakin ne don kare kansu da yan Najeriya - IGP Usman Baba

Baba, wanda ya yi magana da bakin kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya ce umurnin ya zama dole saboda tabbatar da tsaron jami'an da sauran yan Najeriya yayin zaben na 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

IGP din kuma ya ce baya ga kayayyakin, za a bawa jami'an yan sandan sabbin unifom nan take.

Sai dai, ya bukaci jami'an su tabbatar suna fitowa cikin tsafta sanye da dukkan kayayyakinsu domin yin aikinsu bisa doka kafin, yayin da bayan zaben 2023.

Baba ya yi bayanin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa don kawar da laifuka da masu laifi, don haka ake bada muhimmanci kan walwala da jin dadin jami'an da tuni sun fara shiri don zaben, rahoton Premium Times.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

Kara karanta wannan

APC: Abubuwa 3 da Suka Hana a Ga Bola Tinubu a Taron ‘Yan Takaran Shugaban Kasa

"Wannan rabon na zuwa ne a daidai lokacin da aka sayo kayyaki domin jin dadin jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya a daidai lokacin da ake shirin tunkarar babban zaben da ke tafe, don inganta kwarewa da sada zumunta wajen kula da jama'a da kuma murkushe duk wani tashin hankalin jama'a da kuma yin amfani da dabarun zamani na takaita laifuka da aikata laifuka.
"Don haka IGP din ya bada tabbacin cewa rundunar a karkashin jagorancinsa za ta cigaba da samar da abin da ake bukata don habbaka aikin rundunar a dukkan matakai don kawar da laifuka a kasar yayin bada tsaro mafi inganci yayin zaben 2023.
"Kazalika, Sufeta Janar din na yan sanda ya bukaci jami'ansa da su suna da'a da ladabi da mutunta hakkokin mutane yayin aiwatar da ayyukansu."

2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Masu Karya Dokar Zabe A Jihar Kaduna

A wani rahoton, Yekini Adio Ayoku, kwamishinan yan sandan Jihar Kaduna, ya ce rundunarsa ba za ta sassauta wa masu karya dokar zabe ba, rahoton Nigerian Tribune ta.

Kara karanta wannan

Atiku Ya yi kira ga Buhari ya sanya hoton Obasanjo a sabon takardar Naira

Saboda haka, ya gargadi jam'iyyun siyasa da yan takararsu su zama masu biyayya ga dokar zabe idan ba haka ba kuma a kama su a tsare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel