Babu Batun Sanya Iyaka Ga Adadin Kudin da Mutum Zai Mayar Banki Matukar Na Halal Ne, Inji CBN

Babu Batun Sanya Iyaka Ga Adadin Kudin da Mutum Zai Mayar Banki Matukar Na Halal Ne, Inji CBN

  • Babban bankin Najeriya ya warware zare da abawa kan rade-radin da ake yi na adadin kudaden da 'yan Najeriya ka iya ajiyewa a banki
  • Bayan sanar da sauya fasalin kudi a Najeriya, an nemi dukkan 'yan kasar su mayar da N200, N500 da N1,000 zuwa banki
  • Hakazalika, CBN ta yi karin haske kan jita-jitan da ake yadawa na yiwuwar kirkirar sabon nau'in kudi a Najeriya

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya magantu kan jita-jita da ake yadawa na cewa, mutum ba zai iya ajiye wasu adadin kudade ba a asusun banki a yanzu, ya ce babu wani adadi da aka kayyade.

Daraktan kudi na CBN, Ahmed Bello Umar ya bayyana cewa, sam babu batun kayyade wasu miliyoyi, kowa zai iya kawo ko nawa ne kuma ya ajiye a banki ba tare da tsaiko ba matukar kudi ne na halas.

Kara karanta wannan

Daga karshe: CBN ya magantu kan batun cire Ajami a Naira da kuma kirkirar N2,000, N5,000da N10,000

Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi dashi a gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba.

CBN ya magantu kan batun mayar da kudi banki
Babu Batun Sanya Iyaka Ga Adadin Kudin da Mutum Zai Mayar Banki Matukar Na Halal Ne, Inji CBN | Hoto: voahausa.com
Asali: UGC

A hirar ta su, Ahmed ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai wani labari na karya da ke ta yawo cewa, na ba da umarnin duk wanda zai ba da sabon ajiya a banki ba zai ajiye fiye da miliyan 5 ba, idan kuma tsohuwar ajiye ce ba zai wuce miliyan 50 ba a wata.
"Wannan ba haka bane, abin da ma muka yi shine, duk wanda yake da kudi a asusunsa na banki, ko nawa ne ya kawo. Mun ma cire cajin da ake karba na ajiye kudi.
"Idan dai kudinsa ne ya kawo ya sa, babu wani caji da zai biya. Kada ya ji tsoro. Mun san akwai wadanda ke kasuwanci da kudi a hannunsu. Idan ka san kudinka ne ka zo ka sa abinka kawai, babu wani shayi babu kuma wani iyaka da aka yi."

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Mutanen karkara

Da yake karin bayani kan mutanen karkara da ke nesa da bankuna, ya ce suna bukatar kai manyan kudaden banki, amma ba su da bukatar daukar daga 'yan N1,00 ya yi kasa zuwa banki don gudun cikar wa'adi.

Ya shaidawa VOA cewa:

"Mutanen karkara basu da wata damuwa, cikin rukunonin kudade da muke dasu guda takwas, biyar suna nan ana aiki dasu. daga N1,00 zuwa kasa. Saboda ba su da wata damuwa."

Hakazalika, ya yi bayanin cewa, duk da haka suna bukatar kai manyan kudadensu zuwa banki kafin cikar wa'adin lokacin da CBN yace a mayar.

A bangare guda, ya bayyana cewa, ba wai canji ne bankuna za su ke yi, ana son rage adadin kudaden da ke yawo ne a cikin jama'a.

Babu Maganar Cire Rubutun Ajami, Kirkirar N2,000, 5,000, 10,000a Takardar Naira, Inji CBN

A wani labarin, babban bankin Najeriya (CBN) ya magantu kan cece-kuce da jita-jitan da ake yadawa kan kirkirar sabbin kudi a Najeriya, ciki har da N2,000, N5,000 da N10,000.

Kara karanta wannan

Arewa ko Kudu? Peter Obi ya fadi yankin da zai mayar da hankalinsa a kai idan ya gaji Buhari

Rahotanni sun bayyana a kafafen yada labarai na Najeriya kan sauya fasalin kudi a kasar, inda babban bankin da shugaban kasa Buhari suka tabbatar da hakan.

Tun bayan fitowar maganar sauya fasalin kudi, batutuwa suka fara fitowa kan yadda sauyin zai kasance; wasu sun ce za a cire Ajami, wasu kuwa suka ce za a kirkiri gudan N2,000, N5,000 har ma da N10,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel