Dangote Ya Ci Ribar N1.4tr a Rana Daya, Ya Kuma Haura Zuwa Na 71 a Jerin Attajirin Duniya

Dangote Ya Ci Ribar N1.4tr a Rana Daya, Ya Kuma Haura Zuwa Na 71 a Jerin Attajirin Duniya

  • Aliko Dangote ya sake samun karin matsayi a jerin masu kudin duniya na jaridar Bloomberg a ranar Juma'a 4 ga watan Nuwamba
  • Jerin da aka fitar ya nuna Dangote a matsayin na 71 a duniya, inda ya dara matakai biyu na baya; a da yana na 73
  • Wannan kuwa ya faru ne dalilin bunkasar riba da ya samu daga kamfaninsa siminti a kwanakin nan

Habakar riba daga kamfanin simintin Dangote ya sake matsayin mai shi, Alhaji Aliko Dangote, inda ya tsallake matakai biyu a jerin attahiran duniya.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, simintin Dangote ya samar da zunzurutun ribar N332bn a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamban 2022.

Ribar N1.4trn Dangote ya ci a rana daya, inji rahoto
Dangote Ya Ci Ribar N1.4tr a Rana Daya, Ya Kuma Haura Zuwa Na 71 a Jerin Attajirin Duniya | Hoto: bloomberg.com
Asali: UGC

Habakar wannan daraja ta simintin Dangote dai ya jawo tagomashi ga kasuwar hannun jarin Najeriya, inda ta tashi da kauri a kasuwar jiya.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Dangote ya bar na 73, ya zama 71

A cewar rahotanni, tashin daraja da kamfanin simintin ya yi ya kawo karin daraja ga mai kamfanin, domin ya zama na 71 a jerin attajiran duniya daga mataki na 73 na baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da wannan kari da ya samu, an ruwaito cewa, Dangote ya dungura faduwar $788m daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Dangote wanda a yanzu yake kan aikin karasa wata matatar mai mai darajar biliyoyi, shine na daya a kamar kullum a jerin attajiran Afrika tare da zunzurutun kudi $18.3bn.

Elon Musk ne a saman jerin attajiran duniya

Rahoton na Bloomberg ya bayyana cewa, har yanzu dai Elon Musk ne na daya a jerin attajirai, mai bi masa kuwa Bernard Arnault ne, da kuma dan kasar India Gautam Adani da ya banke Jeff Bezos, ya zama na uku.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Bayan sayen Twitter a farashin $44bn, jerin jaridar ya ce akalla Musk ya yi asarar $217m a wata guda, $75.5bn daga farkon shekarar nan zuwa yau.

Matatar Man Dangote Za Ta Fara Samar da Mai Ga Kasar Ghana da Sauran Kasashen Yammacin Afirka

A wani labarin, shigo da kayayyakin man fetur daga kasashen waje na samar da nakasu da illa ga fannin makamashi a kasar Ghana saboda yadda ake tafiyar da harkokin mai a kasar.

Kasar Ghana dai ta kasance daga jerin kasashen dake shigo da danyen man fetur tun shekarar 2010, wannan yasa take da rauni wajen tsayayyen farashin mai kasancewar shigo dashi ake daga Turai.

Business Insider ta ruwaito cewa, shugaban hukumar kula da man fetur a kasar Ghana (NPA), Mustapaha Abdul-Hamid ya ce, fara aikin matatar Dangote zai kawo sauyi sosai a fannin fetur a Ghana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.