Rabiu Kwankwaso Ya Zauna da Jakadun Kasashe 25, Ya Bayyana Dalilin Haduwarsu

Rabiu Kwankwaso Ya Zauna da Jakadun Kasashe 25, Ya Bayyana Dalilin Haduwarsu

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Sakatariyar kungiyar EU, ya hadu Jakadun da ke aiki a Najeriya
  • ‘Dan takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa ya gabatar da manufofinsa ga Misis Samuela Isopi
  • Kwankwaso yace an yi maganar batutuwan da suka shafi Najeriya da kasashen Turai a zamansu

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabar Jakancin kungiyar kasashen Turai na EU a yau.

A shafinsa na Twitter, Rabiu Musa Kwankwaso ya shaida cewa ya zauna da Samuela Isopi da sauran Jakadun kasashen Turai na karkashin kungiyarta.

Mai neman zama shugaban kasar yace an yi zaman ne a sakatariyar kungiyar EU da ke Abuja.

A wajen wannan haduwa da aka yi a ranar Alhamis, ‘Dan siyasar yace ya samu damar tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya da nahiyar Turai.

Kara karanta wannan

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

Rabiu Kwankwaso da ‘yan tawagarsa sun kuma tattauna kan tsare-tsaren huldatayyar kasa-da-kasa kamar yadda yake cikin takardar manufofinsa.

Wadanda aka yi taron da su

‘Yan tawagar tsohon Ministan tsaron tsaron sun hada da tsohon ‘dan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin, Abdullahi Baffa Bichi da Buba Galadima.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Sakatariyar EU Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kasashen da Jakadunsu suka samu halartar wannan zama sun kunshi na Sifen, Hungary, Beljium, Suwidin, Slovakiya, Italiya, Nederland, Girka da Portugal.

Legit.ng Hausa ta kuma fahimci cewa Jakadun kasashen Faransa, Portugal, Jamus, Finland, Denmark da Foland da ke Najeriya su na wajen wannan taron.

Jawabin Rabiu Kwankwaso

"Kafin yanzu, ni da tawagata mun hadu da shugabar jakadancin kungiyar kasashen Turai a Najeriya, Samuela Isopi a yau, tare da sauran jakadun kasashen kungiyar EU a sakatariyar @EU_Commission a garin Abuja.
Haduwar ta bada damar tattaunawa da kyau a kan abin da ya shafi Najeriya da kasashen kungiyar Turai. Mun kuma yi tattaunawa mai tsawo a kan tsare-tsaren huldatayyar kasashen da ke cikin takardar manufofin takararmu.

Kara karanta wannan

Mai Neman Takara Ya Shigar da Karar Jam’iyyar NNPP Saboda An Yi Waje da Sunansa

— RMK

Ziyara zuwa wajen Hidayet Bayrakatar

Kafin nan ‘dan takaran na NNPP a zaben 2023, ya kai wa Jakadan Turkiyya a Najeriya, Hidayet Bayrakatar ziyara a ofishinsa da ke birnin tarayya na Abuja.

Ba mu samu labarin wainar da aka toya a zaman da aka yi a ranar Larabar nan ba. Hadimin ‘dan takarar, Saifullahi Hassan, ya fitar da hotunan zaman a Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng