Majalisar Dattawa Za Ta Titsiye Ministar Kudi Kan N147bn Na Wutar Lantarki

Majalisar Dattawa Za Ta Titsiye Ministar Kudi Kan N147bn Na Wutar Lantarki

  • Ministar kudi za ta sha tuhumar majalisar dattawa kan wasu kudade da ake son sanin inda za a kashe su
  • An ware wasu kudade a ma'aikatar makamashi a Najeriya, sai dai duk masu kare kasafin kudin sun gaza yin bayani
  • Majalisa ta nemi jin ta bakin masu ruwa da tsaki kan aikin wutar lantarkin da ake yi a Mambila shekaru da dama

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar dattawa kan makamashi ya gayyaci ministan kudi, Zainab Ahmed kan wasu kudade N147bn na ayyukan da aka nufi yi a ma'aikatar makamashi ta Najeriya.

Shugaban kwamitin, sanata Gabriel Suswan ne ya bayyana gayyatar ministar a yayin da ma'aikatar makamashi ke kare kasafin kudi a gaban kwamitin, Punch ta ruwaito.

Kwamitin na Suswan ya bayyana damuwa game da manufar kashe kudin a wasu ayyuka, wanda aka gaza ba da bahasi a kai.

Kara karanta wannan

Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure

Majalisa ta gayyaci ministar kudi kan wasu kudade
Majalisar dattawa za ta titisye ministar kudi kan N147bn na wutar lantarki | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake bayyana rashin fahimtar inda aka shirya kashe kudaden, Suswan ya bukaci ganin ministan kudi ta zo ta yi bayanin yadda za a kashe N147bn na kasafin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Muna gayyatar minstar kudi ta zo ta yi mana bayani. Ana saka kudin a kasafin kudi a kowace shekara, ba tare da bayyana ainihin manufarsa ba."

Ma'aikatar makamashi ta Najeriya ta gabatar da jumillar N250bn na kasafin kudin 2023 a madadin ma'aikatar.

Hukumar EFCC Na Binciken Aikin Wutar Lantarki Ta Mambilla, Inji Ministan Makamashi

A tun farko, kwamitin majalisar dattawa ta Najeriya kan wutar lantarki ya bayyana aikin samar da makamashi na Mambilla a matsayin yaudara, duk kuwa da tanadin kasafin kudi na shekara-shekara da gwamnati ke zubawa kullum.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar EFCC ke kan bincikenta na yadda ake gudanar da aikin, in ji ministan makamashi Engr. Abubakar D. Aliyu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa Sun Fadawa Buhari Masu Kawo Tasgaro Wajen Yakar Rashin Gaskiya

Aikin makamashin Mambila dai sananne ne a gwamnatin Buhari, kuma an nufi samar da wutar lantarki da ta kai megawatts 3,050 idan aka kammala, wanda a yanzu ake kyautata zaton ana ci gaba da aikin.

Idan aka kammala shi, ana sa ran ya zama hanyar samar da wutar lantarki mafi girma a Najeriya, kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a Afrika.

Buhari Ya Gaza, Ya Kamata Duk Dan Najeriya Ya Nemi Makami, Inji Dan Majalisar PDP

A wani labarin, Toby Okechukwu, mamban majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam'iyyar PDP ya bukaci gwamnatin kasar nan ta ba 'yan kasa damar mallakar makamai don kare kawunansu.

Ya bayyana hakan ne a duba da ya yi da karuwar ta'azzarar lamarin tsaro a Najeriya da kuma yadda gwamnati ta gaza kawo mafita.

Dan majalisar da ya taso daga jihar Enugu ya bayyana hakan ne a wata tattauna da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.