Zaben 2023: Tamkar Wike, Babban Gwamnan APC Ya Dauki Kwakwarar Mataki Kan Jam'iyyun Siyasa
- Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya dauki matakin ganin ba a siyasantar da makarantun gwamnati ba
- Gabanin babban zaben 2023, Gwamna Umahi ya haramta amfani da makarantun jihar don yin kamfen din siyasa
- Jigon na jam'iyyar APC mai mulki ya ce kafin a yi wani rali, sai an nemi izini daga Ma'aikatar Ilimi kuma a gabatar da shi
Jihar Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya haramta yin kamfen din siyasa a makarantun gwamnati na jihar.
Mista Umahi ya kuma haramta wa masu acaba aiki daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe saboda magance rashin tsaro a jihar.
Dole jam'iyyun siyasa su nemi izini, In Ji Umahi
Gwamnan ya sanar da haramcin ne a Abakaliki a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba, a wurin taron masu ruwa da tsaki kan gudumawar yan jiha da tuntuba don kasafin 2023, Rivers Mirror ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Taron ta kuma tattauna batun gurbatar da muhalli a Najeriya da kidayar shekarar 2023.
Mista Umahi ya ce dole jam'iyyun siyasa su nemi izini daga kwamishinan ilimi na jihar kafin yin tarukan siyasa a makarantu.
Ya ce:
"In son sanarwa karara cewa daga ranar 1 ga watan Nuwamba, kafin jam'iyyar siyasa ta yi taro a makarantun frimari ko sakandare, dole su nemi izini daga Ma'aikatar Ilimi.
"Ba mu yarda a yi wani kamfen ba a makarantun gwamnati, wannan shine matsayar mu.
"Ba mu son a rika bata mana kayayyaki a makarantu da sunan kamfen. Ba mu san mutane su tafi wurin suna bahaya a kusa da harabar makarantu.
"Muna son hana lalata kayayyakin makarantun mu."
Rikici Ya Kara Tsanani, Gwamna Wike Ya Sha Alwashin Ba Zai Bar Arewa Ta Mamaye Komai a PDP Ba
Yayin da rikici ke kara kamari a jam'iyyar PDP, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sha alwashin cewa, ba zai bari 'yan Arewa su ci gaba da mamaye manyan kujeru a jam'iyyar ba.
Wike ya yi watsi da tsarin da jam’iyyar ke kai a yanzu haka inda manyan masu rike da mukamai suka fito daga yankin arewacin kasar.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu; dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Aminu Tambuwal duk 'yan arewa ne.
Asali: Legit.ng