Sarkakiya: Mafi yawan mayakan kungiyar Boko Haram ba musulmai ba ne - Sabon rahoto

Sarkakiya: Mafi yawan mayakan kungiyar Boko Haram ba musulmai ba ne - Sabon rahoto

Wani sabon rahoto mai sarkakiya da a halin yanzu ya kara daurewa mutane kai shine yadda yayi bayanin cewa mafi yawancin mayakan Boko Haram ba musulmai bane ba, kiristoci ne kamar dai yadda ya bayyana.

Shi dai wannan rahoton kafar labarai ta Radiyon kasar Faransa ne ta wallafa shi kuma mun samu haka ne daga jaridar Daily post ta Najeriya.

Sarkakiya: Mafi yawan mayakan kungiyar Boko Haram ba musulmai ba ne - Sabon rahoto
Sarkakiya: Mafi yawan mayakan kungiyar Boko Haram ba musulmai ba ne - Sabon rahoto

KU KARANTA: Babban malamin addini ya kashe mabiyan sa 3

Legit.ng ta samu cewa an bayyana kai hare-haren da kungiyar ke yi a matsayin sana'a ne sannan kuma ba su da wasu kebabbun mutane da suke so lallai sai su za su kai masu harin don haka su kan dauki hayar ko ma wa ya tari gaban su.

Wannan ne dai ya sanya wasu mutane a kasar ta Najeriya suka yi nazari game da lamarin inda kuma suka gano cewa 'yan kungiyar sukan yi anfani da kiristoci da dama wajen kai hare-haren su musamman ma gnin cewa tamkar sana'a suka dauki hakan.

Kamar dai yadda binciken ya nuna, har ila yau an tattauna da wasu kiristocin da aka kama suna kokarin kai hari inda suka bayyana cewa rashin aikin yi ne ya sanya su karbar tayin kai harin daga kungiyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng