CBN Bata Ajiye Batun Gabatar da Gudan Naira 5,000 Ba, Inji Sanusi II

CBN Bata Ajiye Batun Gabatar da Gudan Naira 5,000 Ba, Inji Sanusi II

  • Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa, Babban Bankin Najeriya zai ci gaba wajen kirkirar takardar N5,000 guda a Najeriya
  • Sanusi ya bayyana matsayar CBN kan batun cire Ajami a jikin kudaden da aka ce Najeriya za ta sauya kamanninsu
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da cece-kuce tun bayan da gwamnati ta sanar da yunkurin sauya kamannin Naira

Najeriya - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na kan bakanta na kirkirar gudan N5,000 a nan gaba.

Babban bankin Najeriya ya fara kawo batun yin gudan N5,000 a shekarar 2012, lokacin da Sanusi yake matsayin gwamna, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar, rahoton The Nation.

Sanusi ya magantu kan batun kirkirar sabon kudi
CBN Bata Ajiye Batun Gabatar da Gudan Naira 5,000 Ba, Inji Sanusi II | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Masana tattalin arziki da dama a kasar sun yi ta tsokacin cewa, kawo gudan N5,000 zai dagula lamarin tattalin arzikin kasar, kuma zai kawo tsadar kayayyaki.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 Dake nuna Peter Obi Ba zai Samu Nasara A Zaben 2023, Fitch Solutions

Dalilin da Sanusi ya bayar na kirkirar N5,000

A wancan lokacin, Sanusi ya kafa hujja da cewa, a kasashe kamar Singapore, Germany da Japan, manyan kudadensu sune 10,000 SGD, Yuro 500 da Yen 10,000 bi da bi, Legit.ng ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma bayyana cewa, wadancan kudade na goyayya da dala wajen daraja, kuma akwai sauki a fannin tsadar kayayyaki a kasashen.

A cewar Sanusi, kirkirar manyan kudade kamar gudan N5,000 zai taimakawa CBN wajen tabbatar da tsarinsa na rage yawaitar kudi a hannun jama'a, kasancewar tarkacen kudade kanana za su yi kadan idan manyan kudi ne suka fi yawa.

Hakazalika, ya yi tsokaci kan jita-jitar da ake yadawa a Najeriya game da sauyin kamannin kudi da CBN yake shirin yi kwanan nan.

Maganar Shirin Cire Ajami daga Takardun Kudin Najeriya Ba Gaskiya ba ne

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

A bangare guda, tsohon gwamnan na babban bankin, ya fito ya yi magana game da jita-jitar cire rubutun Ajami daga takardun Naira.

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a shafinsa na Twitter, an ji Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana karyata rade-radin da ke yawo.

Ganin har wasu malaman addini sun fara fashin-baki a kan lamarin alhali bai tabbata ba, Sanusi II ya yi kira ga malaman su daina aiki da jita-jita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel