CBN Bata Ajiye Batun Gabatar da Gudan Naira 5,000 Ba, Inji Sanusi II
- Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa, Babban Bankin Najeriya zai ci gaba wajen kirkirar takardar N5,000 guda a Najeriya
- Sanusi ya bayyana matsayar CBN kan batun cire Ajami a jikin kudaden da aka ce Najeriya za ta sauya kamanninsu
- 'Yan Najeriya na ci gaba da cece-kuce tun bayan da gwamnati ta sanar da yunkurin sauya kamannin Naira
Najeriya - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na kan bakanta na kirkirar gudan N5,000 a nan gaba.
Babban bankin Najeriya ya fara kawo batun yin gudan N5,000 a shekarar 2012, lokacin da Sanusi yake matsayin gwamna, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar, rahoton The Nation.
Masana tattalin arziki da dama a kasar sun yi ta tsokacin cewa, kawo gudan N5,000 zai dagula lamarin tattalin arzikin kasar, kuma zai kawo tsadar kayayyaki.
Dalilin da Sanusi ya bayar na kirkirar N5,000
A wancan lokacin, Sanusi ya kafa hujja da cewa, a kasashe kamar Singapore, Germany da Japan, manyan kudadensu sune 10,000 SGD, Yuro 500 da Yen 10,000 bi da bi, Legit.ng ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bayyana cewa, wadancan kudade na goyayya da dala wajen daraja, kuma akwai sauki a fannin tsadar kayayyaki a kasashen.
A cewar Sanusi, kirkirar manyan kudade kamar gudan N5,000 zai taimakawa CBN wajen tabbatar da tsarinsa na rage yawaitar kudi a hannun jama'a, kasancewar tarkacen kudade kanana za su yi kadan idan manyan kudi ne suka fi yawa.
Hakazalika, ya yi tsokaci kan jita-jitar da ake yadawa a Najeriya game da sauyin kamannin kudi da CBN yake shirin yi kwanan nan.
Maganar Shirin Cire Ajami daga Takardun Kudin Najeriya Ba Gaskiya ba ne
A bangare guda, tsohon gwamnan na babban bankin, ya fito ya yi magana game da jita-jitar cire rubutun Ajami daga takardun Naira.
A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a shafinsa na Twitter, an ji Mai martaba Muhammadu Sanusi II yana karyata rade-radin da ke yawo.
Ganin har wasu malaman addini sun fara fashin-baki a kan lamarin alhali bai tabbata ba, Sanusi II ya yi kira ga malaman su daina aiki da jita-jita.
Asali: Legit.ng