Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini A Najeriya Rasuwa

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini A Najeriya Rasuwa

  • Most Rabaran Bamisebi Olumakaiye, Archbishop na Ecclesiastical Province na Legas, ya rasu
  • Wata sanarwa da cocin ta fitar a nuna cewa Most Rabaran Olumakaiye ya rasu a daren ranar Lahadi, 31 ga watan Oktoba yana da shekaru 53
  • Cocin na reshen Legas ta ce nan bada dadewa ba za a fitar da tsarin yadda za a yi jana'isarsa

Legas, Najeriya - Cocin Anglican, reshen jihar Legas, ta sanar da rasuwar Archbishop na Ecclesiastical Province na Legas, Most Rabaran Bamisebi Olumakaiye.

An sanar da rasuwar Most Rabaran Olumakaiye ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakatare, Ven. Segun Ladeinde; da Chancellor, Mai shari'a Adedayo Oyebanji, Channels TV ta rahoto.

Humphrey
Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini A Najeriya Rasuwa. Hoto: @Naija_PR, @Remy_0007
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

Legit.ng ta tattaro cewa malamin addinin ya rasu a yammacin ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba yana da shekaru 53.

Wanene Humphrey Bamisebi Olumakaiye?

An nada Olumakaiye matsayin Bishop na Legas a ranar 30 ga watan Yulin 2018, a Nuwamban 2021 aka gabatar da shi matsayin Archbishop na Ecclesiastical na Legas.

Sanarwar ta ce:

"An samu manyan cigaba karkashin jagorancin bishop din wadanda za a iya gani a fili da na boye cikin kankanin lokacin da ya yi a Legas, wanda muke alfahari da su.
"Za mu cigaba da bada bayani a yayin da ake shirye-shiryen jana'izarsa."

Yaya Humphrey Bamisebi Olumakaiye ya rasu

Olumakaiye ya shafe watanni shida yana fama da rashin lafiya, a cewar The Nation.

An ce an kai shi kasar waje don magani a watan da ya gabata amma ba a samu cigaba sosai a lafiyarsa ba.

Rasuwarsa shine na uku a cocin Anglican na Najeriya, cikin watanni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Rt. Rabaran Joly Oyekpen, Bishop din Akoko Edo, ya rasu a ranar 29 ga watan Agusta, yayin da Rt. Rabaran David Obiosa na Ndokwa ya rasu kimanin mako daya da wuce.

Allah ya yi wa Mahaifin Sanatan Najeriya Rasuwa

Alhaji Ali Buba Ndume, Mahaifin sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume ya rigamu gidan gaskiya.

Sanatan da kanshi ya bayyana haka a wani jawabi da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata.

Ya kara da bayyana cewa za'a yi jana'izar mahaifin nashi yau Talata a Maiduguri jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel