Tarihi 5 da Messi ya kafa bayan da Barcelona ta suburbudi Real Madrid
- Yanzu dai Messi shine kan gaba wajen zura kwallaye a wasa tsakanin Real Madrid da Barcelona
- Dan wasan Messi ya zura kwallo a ragar Real Madrid a jiya
- Messi ya taimakawa Barcelona wajen gyara zaman ta a saman teburin Laliga
Shahararren dan wasan kwallon kafar nan na kungiyar Barcelona dake kasar Sifen kuma dan asalin kasar Ajantina watau Lionel Messi a jiya ya taimakawa kungiyar sa wajen suburbudar kungiyar Real Madrid 3 da 0.
Legit.ng ta samu cewa shi dai dan wasan ya zura tasa kwallon ce a wani bugun finarati da a wasan jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci bayan da wani dan wasan baya na Real Madrid mai suna Carvajal ya taba kwallon da hannu..
Yanzu dai dan wasan Messi shine wanda yafi kowa kwallo a karawa tsakanin kungiyar Real Madrid da Barcelona.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng