Dalar Amurka ta Kara Tsinkewa a Kasuwar Canji, N800 Ba Za Ta Iya Sayen $1 ba

Dalar Amurka ta Kara Tsinkewa a Kasuwar Canji, N800 Ba Za Ta Iya Sayen $1 ba

  • Tun da Gwamnan CBN ya bada sanarwar za a canza takardun kudi, Naira take cigaba da sukurkucewa
  • Da jin bayanin Godwin Emefiele, mutane suka rika fito da Nairori domin su canza su da kudin kasar waje
  • Wannan ya taimaka wajen kara wahalar samun Dalar Amurka, hakan yana nufin Naira za ta rage daraja

Abuja - Darajar Naira tana cigaba da sauka kasa ne kamar yadda cinikin da ake yi a kasuwar canji suka tabbatar a farkon makon nan.

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar a ranar 1 ga watan Nuwamba 2022, an ji cewa Dalar Amurka tana cigaba da yin riba a kan Naira.

A ranar Litinin dinnan, sai da ‘yan canji suka saida Dalar Amurka daya a kan N815 a garin Legas, kusan abin da ba a taba jin labari ba.

Kara karanta wannan

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

Lamarin ya fi haka jagwalgwalewa a birnin tarayya Abuja, domin ‘yan canji sun saida $1 a kan N818 kafin a tashi daga kasuwa a jiya.

Canjin kudi ya jawo haka?

Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna cewa Naira tana kara sukurkuce a sakamakon sanarwar da gwamnan babban banki ya bada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Godwin Emefiele yace za a canza manyan takardun kudi, don haka wadanda suka boye Naira suke ta fito da su domin su canza a kasuwa.

Banki
Kudi a banki Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yawan neman Dalar Amurka da ake yi a kasuwar canjin ya jawo farashinsa ya tashi, hakan ya na nufin Naira za ta rasa kimar ta a Najeriya.

A lokacin da Godwin Emefiele ya bada wannan sanarwa, ana canza Dalar Amurka ne a kan N765, kawo yanzu Naira ta rasa fiye da N50 a BDC.

Ana neman Daloli, an rasa

Kara karanta wannan

Yadda Mutum 306 Suka Samu Tagomashi Daga Kudin Zakkah, An Raba Masu N55m

‘Yan canji sun zama gwal a halin yanzu, jaridar tace nemansu ake yi ido rufe a unguwar Wuse Zone 4 a Abuja domin a samu Daloli.

Wani ‘dan jarida ya fake da sunan yana neman sayen $10, 000, amma ba a samu wani ‘dan canji da yake da wadannan Daloli a hannunsa ba.

Majiyar tace jami’an EFCC na zuwa Bureau De Change domin kama wadanda aka samu da Daloli, hakan ya sa abin ya kara yin wahala.

Za a lalata N6tr a Najeriya

Rahoton da aka fitar a jiya ya nuna Bincike ya nuna Bankin CBN zai lalata takardun kudi na kimanin N6, 000, 000, 000, 000 a shekaru takwas.

Babban bankin kasar yana bata duk kudin da suka tsufa ko suka yi rashin kyawun gani, sai a sake buga wasu sababbi da za a rika kashewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng