Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutum `10 A Zamfara, Sun Bukaci A Biya N20m Kudin Fansa
- Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 10 a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara
- 'Yan bindigar da suka farmaki Dogondaji da Kazauda sun nemi a biya naira miliyan 20 kudin fansar mutanen da ke tsare a hannunsu
- Rundunar yan sandar jihar ta bayyana cewa za ta kaddamar da bincike kan lamarin
Zamfara - Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 10 a wasu garuruwa biyu da ke kauyukan Dogondaji da Kazauda a yakin Wanke, karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Maharan sun kuma bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar mutanen.
A hira da yayi da jaridar Punch ta wayar tarho, wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Musa ya ce mutum shida aka sace a kauyensa na Kazauda yayin da aka sace hudu a kauyen Dogondaji inda suka bukaci naira miliyan 2 kan kowanne.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yan bindigar sun bukaci naira miliyan 2 kan kowani mutum kafin su sako mutane 10 da ke hannunsu gaba daya suna bukatar naira miliyan 20."
Musa ya kara da cewar al'ummar garinsa da ke Kazauda sun yi nasarar tara naira miliyan 1.1 ne kadai yayin da yan Dogondaji basu hada komai ba tukuna.
Ya ce:
"Mun yi nasarar tara naira miliyan 1.1 ta hanyar gudunmawar da wasunmu suka bayar kuma mun sanar da yan ta'addan game da hakan.
"Amma sun fada mana cewa ba za su karbi kasa da naira miliyan 2 ba kan kowani mutum da ke hannunsu."
Musa ya roki hukumomi da su kawo masu dauki sannan su taimaka wajen ceto mutanen da aka sace.
Da aka tuntube shi ta wayar tarho, kakakin yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce za su binciki lamarin amma bai yi karin bayani ba, rahoton Vanguard.
Ya ce:
"Za mu binciki lamarin."
Yan Sanda Sun Dakile Hare-Haren Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara
A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sandan Zamfara ta dakile hare-haren yan bindiga a kananan hukumomi hudu da ke jihar sannan ta ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su, jaridar Punch ta rahoto.
A wata sanarwa daga kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce yan bindigar sun so kai hari kan wasu kauyuka a kananan hukumomin Maru, Bungudu, Tsafe da Bukkuyum amma aka dakile shi bayan samun bayanan sirri.
Asali: Legit.ng