Mata za su samu tallafin akuyoyi da bunsuru 47,544 daga gwamnatin jihar Jigawa
Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa za ta rabawa mata 15,848 akuyoyi 47,544 a watan Yunin 2019 a karkashin shirin kiwon akuyoyi na Bankin bayar da bashi ga masu karamin karfi na jihar.
Badaru wanda ya yi magana da manema labarai a ranar Litinin a Dutse ya ce wannan tallafin yana cikin shirin jihar na tallafawa al'umma ta fanin kiwon dabobi.
A cewarsa, mata 8,428 sun karbi akuyoyi 25,284 a karkashin shirin a shekarar 2018.
DUBA WANNAN: An sako Buhari a gaba a kan satar basira a salon kamfen dinsa
Ya ce shirin bayar da tallafin dabobin shine shirin bayar da bashi da mafi nasara a jihar inda ya ce 92% suna cigaba da kiwon kuma 79% sun biya bashin da aka basu.
A fanin noma kuma, gwamnan ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo ya janyo hankalin masu saka hannun jari zuwa jihar daga gida Najeriya da ma kasashen waje.
"A halin yanzu, Dangote yana gina kamfanin sarrafa shinkafa a Kaugama da za ta rika samar da ton 280 na shinkafa a kowanne shekar idan an kammala.
"Kazalika, kamfanin Lee na saka hannun jari wajen noman rake a fili mai girman hecta 12,000 domin samar da raken da kamfanin ta zai rika samar da suga ton 120,000 a duk shekara.
"Kamfanin kuma zai rika samar wasu abubuwa masu amfani kamar taki ga manoma, wutar lantarki, mazarkwaila da dankulen maggi," inji Badaru.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng