Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Kawo Dalilin Goyon Bayan CBN Kan Buga Sabon Kudi

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Kawo Dalilin Goyon Bayan CBN Kan Buga Sabon Kudi

  • Kingsley Moghalu ya yabi Gwamnan CBN a kan maganar sake buga takardun N200, N500 da N1000
  • Tsohon mataimakin gwamnan CBN din yace akwai bukatar a canza kudin idan aka duba lamarin tsaro
  • Farfesan yace babban bankin Najeriya yana da damar da zai canza kudi ko ba da sanin Ministar tattali ba

Lagos - Farfesa Kingsley Moghalu yace yana goyon bayan buga sababbin takardun Naira da babban bankin Najeriya watau CBN zai yi a Najeriya.

A wani rahoto da gidan talabijin Channels suka fitar, an ji Kingsley Moghalu yana yabon wannan mataki da gwamnan babban banki na kasa ya dauka.

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN yace idan 80% na takardun Naira da ake da su ba su hannun bankuna kamar yadda aka fada, lallai akwai matsala.

Masanin tattalin arzikin ya yi magana a shafin Twitter, yace matakin da aka dauka ya yi daidai, sai dai ba dole ba ne ya yi maganin hauhawar farashi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

Har yanzu akwai sauran aiki

Sahelian Times ta rahoto Farfesa Moghalu yana cewa buga sababbin kudin zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro da ya yi katutu a yau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da amfanin da za a gani, Moghalu yana da ra’ayin cewa wa’adin da Gwamnan CBN ya bada domin mutane su maida kudi zuwa banki ya yi kadan.

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN
Kingsley Moghalu a wajen wani taro Hoto: @MoghaluKingsley
Asali: Twitter

Dalilin da ya bada kuwa shi ne, akwai wasu dalilai dabam da ke jawo tashin farashin kaya, daga ciki akwai karancin kudin kasar waje da ake fama da shi.

Baya ga haka, masanin yace matakin zai iya jawo karanci da wahalar kayan abinci a Najeriya.

Sabanin CBN da Ministar kudi

A yau kuma, Legit.ng Hausa ta bibiyi shafin Farfesan, ta ji yana karin haske a kan sabanin da aka samu tsakanin Ministar kudi da Gwamnan babban banki.

Kara karanta wannan

Malami Ya Bayyana Dalilai 4 da Yasa FG Ke Cigaba da Garkame Nnamdi Kanu

Moghalu yake cewa ba dole sai Godwin Emefiele ya nemi izinin Zainab Shamsuna kafin a iya buga kudi ba, yace wannan aikin shugaban kasa ne kurum.

"Ka da bayanin da Zainab Ahmed tayi wa majalisa cewa ba ta san CBN za ta sake buga kudi ba, ya yaudari wani har ya dauka dole sai CBN ta sanar da ita.
Bankin na bukatar izinin Shugaba Muhammadu Buhari kadai ne wajen irin wannan aikin."

Tasirin canza kudi

A baya an rahoto wani masanin tattalin arziki, Temitope Omosuyi yace duk wani mai boye kudi zai kai su banki run da gwamnan CBN ya bada wannan sanarwa.

Masana sun ce idan CBN ya iya tattara kan kudin da ake da su, ana sa ran a shawo kan yadda farashin kaya ke tashi, wasu kuma suna ganin akasin haka za ta faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng