2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru
An yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a Najeriya, Vanguard ta rahoto.
Legit.ng ta rahoto cewa kamfanin Fitch Solutions Country Risk and Industry Research ta yi wannan hasashen a sabuwar rahoton ta.
Kamfanin, wanda wani reshe ne na Fitch Ratings, ƙungiyar ƙididdiga ta ƙasa da ƙasa, kuma ta kara da cewa nasarar Tinubu zai janyo rashin zaman lafiya da zanga-zanga saboda tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyarsa ta yi.
Rahoton ya ce:
"Muna kan ra'ayinmu cewa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyya mai mulki shine dan takarar da ya fi sauran damar yin nasara saboda rabuwar kai a jam'iyyar hammaya zai amfani APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ta yi wu zanga-zanga da rashin zaman lafiya zai karu bayan nasarar Tinubu tunda wannan zai kawo karshen karba-karba da aka sabi yi tsakanin musulmi da kirista a shugabancin kasa.
"Tun da Najeriya ta dawo demokradiyya a 1999, akwai wani yarjejeniya duk da cewa a rubutaciyya bane na karba-karba tsakanin jihohin arewa da kudu, da musulmi da kirista.
"Nasarar Tinubu na iya karya wannan al'adar kuma na iya rura wutar wariyya da kiristoci ke zargin ana musu."
2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili
Shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard na kasa, Mr Sunday Asefon, a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba, a Abuja, ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya zu zabi Tinubu Shetima a zaben shugaban kasa na 2023.
Asefon ya yi wannan alkawarin ne yayin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguards, The Nation ta rahoto.
Asefon, tsohon shugaba na kasa na kungiyar daliban Najeriya, (NANS), ya ce kungiyar za ta zama babban tafiya ta dalibai da zata taimaka wurin tabbatar da nasarar 'Renewed Hope'.
Asali: Legit.ng