Wani Bawan Allah Mai Shekara 45 Ya Mutu Cikin Rijiya A Kano

Wani Bawan Allah Mai Shekara 45 Ya Mutu Cikin Rijiya A Kano

  • Mutanen garin Dan Dutse a karamar hukumar Bichi na jihar Kano suna juyayin rashin wani mazanin garin
  • Habibu Mu'azu, wani mazaunin Dan Dutse mai shekaru 45 ya riga mu gidan gaskiya bayan ya fada rijiya
  • Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kwana-kwana na Kano ya ce tawagar cetonsu ta ciro mammacin daga rijiyar amma baya numfashi, daga bisani aka tabbatar ya rasu

Jihar Kano - Wani mutum mai shekara 45, mai suna Habibu Mu'azu, ya fada cikin rijiya ya rasu a Yan Dutse, karamar hukumar Bichi a Jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.

Hakan na cikin wata sanarwa ne da mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Juma'a.

Taswirar Jihar Kano
Wani Bawan Allah Mai Shekara 45 Ya Mutu Cikin Rijiya A Kano. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A cewar sanarwar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

"Mun samu kiran neman daukin gaggawa misalin karfe 7.44 na safiyar ranar Juma'a daga Sunusi Abubakar cewa wani mutum ya fada rijiya kuma nan take muka tura tawagarmu na ceto zuwa wurin.
"An ciro Mu'azu daga rijiyar baya numfashi kuma daga bisani aka tabbatar ya rasu, an mika gawarsa ga mai unguwar Yan Dutse, Bello Usman."

Kakakin hukumar kwana-kwanan ya kara da cewa an fara bincike a kan lamarin.

Kano: Mahaifi Da Dansa Sun Nutse A Cikin Rijiya Sun Mutu

Wani mutum dan shekara 60 mai suna Malam Bala da dansa, Sanusi Bala, ɗan shekara 35 sun mutu a rijiya a Sabon Garin Bauchi, karamar hukumar Wudil na Jihar Kano a lokacin da suke yashe rijiyar.

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ba Wa Cocin Katolika Kyautan Naira Miliyan 20 A Wata Jihar Arewa

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru a safiyar ranar Talata.

Yarinya Ƴar Shekara 4 Ta Faɗa Rijiya a Kano, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar yarinya yar shekara hudu, Amina Garba, bayan ta fada rijiya a Kofar Waika, da ke kallon Masallacin Karmawi, a karamar hukumar Ungoggo a jihar.

Kakakin hukumar, Alh Saminu Abdullahi, ya ce hukumar ta Kofar Nassarawa ta samu kiran neman dauki misalin karfe 2.05 na ranar Litinin daga wani Alkasim Ibrahim, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel