Kano: Mahaifi Da Dansa Sun Nutse A Cikin Rijiya Sun Mutu

Kano: Mahaifi Da Dansa Sun Nutse A Cikin Rijiya Sun Mutu

  • Wani mahaifi mai suna Malam Bala da dansa Sunusi Bala sun yi mutuwar shahada a yayin da suka makale cikin rijiya a Kano
  • An kira Malam Bala da dansa ne su taho su yashe wani rijiya a unguwar Sabon Garin Bauchi, karamar hukumar Wudil a yayin da lamarin ya faru
  • Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano ya tabbatar da rasuwarsu yana mai cewa rashin iskar da za su shaka a lokacin da suka makale ya yi sanadin rasuwarsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Wani mutum dan shekara 60 mai suna Malam Bala da dansa, Sanusi Bala, ɗan shekara 35 sun mutu a rijiya a Sabon Garin Bauchi, karamar hukumar Wudil na Jihar Kano a lokacin da suke yashe rijiyar.

Taswirar Kano
Kano: Mahaifi da ɗansa sun nutse a cikin rijiya sun mutu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Terhemen Anongo: Dalibin da Ya Bar Karatun Likitanci a Aji 5, Ya kare a Turin Baro

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru a safiyar ranar Talata.

Abdullahi ya ce:

"Mun samu kiran neman dauki a ofishin mu na Wudil misalin ƙarfe 10.30 na safe daga wani Isma'ila Idris cewa wasu mutane biyu sun makale cikin rijiya. Nan take muka aika tawagar mu na ceto suka isa wurin misalin ƙarfe 11.33 na safe.
"An kira wani mutum da dansa su yashe rijiya. Sun yi nasarar yashe rijiyar. Amma, yaron ya koma cikin rijiyar don kwashe kasar a lokacin ya makale kuma ya mutu saboda rashin iska.
"Mahaifinsa shima ya shiga rijiyar don ya ceto shi yayin da shima ya makale kuma ya rasu saboda rashin iska a cikin rijiyar."

Sanarwar ta ce an fito da mutanen biyu daga cikin rijiyar a sume kuma daga bisani aka tabbatar sun rasu.

An mika gawarsu ga Sufeta Felix Gowok na ofishin yan sanda na Wudil Model Police Station.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: 'Yan Shi'a 6 da Jami'an Tsaro Suka Bindige a Zaria

Ya bayyana cewa rashin iskar shaka ne ya yi sanadin mutuwarsu.

Mata 13 Sun Mutu Bayan Rufta Wa Cikin Rijiya a Wurin Bikin Ɗaurin Aure

A wani rahoton, kun ji cewa manyan mata da yara mata 13 sun mutu bayan tsautsayi ya yi sanadi sun fada rijiya yayin bikin aure a arewacin India, yan sanda suka sanar a ranar Alhamis, rahoton Channels TV.

Wadanda abin ya faru da su suna zaune ne a kan wani murfin karfe da ya rufe rijiyar a ranar Laraba kwatsam sai ya rufta, babban jami'in dan sanda Akhil Kumar ya shaidawa manema labarai a Kushinagar, Jihar Uttar Pradesh.

Channels TV ta rahoto cewa Babban alkakin yankin, S. Rajalingam ya ce tsohuwar rijiya ce don haka ta kasa dauka nauyin wadanda suka zauna a murfin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel