Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022
- EFCC tayi shari’a da mutane 2, 847 zuwa yanzu a shekarar nan, kuma Alkali ya zartar masu da hukunci
- Wannan bayani ya fito daga bakin shugaban hukumar a lokacin da ya je gaban ‘yan majalisar dattawa
- Abdulrasheed Bawa yace mafi yawan wadanda su ka samu da laifin damfarar Bayin Allah, duk matasa ne
Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya, tayi nasarar daure mutane 2, 847 da suka aikata laifuffukan damfara a shekarar bana.
Shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa ya yi wannan bayani yayin da bayyana a gaban majalisa. Jaridar Premium Times ta kawo wannan rahoto.
Abdulrasheed Bawa ya zauna da kwamitin yaki da rashin gaskiya na majalisar dattawa domin ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2022/23.
Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani
An yi wannan zama ne a bayan labule, sai bayan nan Bawa ya samu lokaci ya zanta da ‘yan jarida.
A cikin mutane kusan 3, 000 da aka yankewa hukunci a shekarar nan, Bawa yace mafi yawancinsu matasa ne da ya kamata su marawa hukumar baya.
Shugaban na EFCC yace masu danyen aikin su na bata sunan Najeriya a idon Duniya, yace doka ta ba su dama su yaki damfara da masu zamba cikin aminci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Ina kira gare su da su daina yin wadannan aika-aika a irin wannan gabar lokaci da kasar nan ta ke ciki.
Ana shirye-shiryen zabe, gwamnati tana bakin kokari na ganin tattalin arzikin Najeriya ya dawo daidai."
- Abdulrasheed Bawa
Canjin kudi daidai ne - EFCC
Da yake jawabi, shugaban hukumar ta EFCC ya yabi babban bankin kasa na CBN bisa matakin da ya dauka na buga sababbin kudi, yace hakan zai taimaka.
“Abin maraba ne da za a buga sababbin kudi. Ta ya za ku iya kawo tsarin kudi da zai yi aiki alhali babu yadda ku ka iya da 85% na kudin kasarku.”
“Na tabbata za a gano masu rike kudin nan ko ta hanyar halal ne ko ta haram, za mu iya sa ido, daga nan sai doka tayi aiki yadda ya kamata.”
- Abdulrasheed Bawa
Rahoton ya tuna da cewa a shekarar da ta wuce, EFCC ta samu nasarar da ta fi kowace a tarihin kafuwarta, aka yankewa mutane 2, 220 hukunci a kotu.
EFCC ta 'matsawa' matasa
A baya an ji labari, jami’an EFCC sun tasa ‘yan damfara da ake kira da ‘yan yahoo-yahoo a gaba, har ana zarginsu da watsi da sauran manyan barayin kasar.
Wannan ya jawo matasa suka yi zanga-zanga a garin Ibadan domin su nuna adawarsu ga aikin EFCC, suka yi kira ga gwamnati ta rusa hukumar gaba daya.
Asali: Legit.ng