An samu karin kasashe da suka gano yiwuwar kai hare-hare a Abuja da Jihohi 22
- Gwamnatocin kasashen ketare sun goyi bayan Amurka da Ingila a kan barazanar tsaro a Najeriya
- Jakadancin Jamus, Bulgariya da Denmark sun bada shawarar a guji zuwa Najeriya sai ya zama dole
- An sa jihohin Delta, Akwa Ibom, Ribas, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto a cikin masu hadari
Abuja - Gwamnatocin Jamus, Bulgariya, Ireland da Denmark duk sun ja-kunnen mutanensu a kan yin tafiya zuwa Najeriya idan babu kwakkwaran dalili.
Daily Trust tace wadannan kasashe sun gano yiwuwar ‘yan ta’adda su kai hare-hare. Amma Ministan yada labarai yayi watsi da wannan barazanar tun tuni.
Rahoton da muka samu a ranar Juma’ar nan shi ne, bayan zama da Jakadun Amurka suka yi da na sauran kasashen ketare, sun fahimci hadarin da ake ciki.
Hukumomin Amurka sun nunawa kasashen bayanan da ke nuna ana fuskantar barazana. Wannan ya sa aka samu kasashen da ke goyon bayan matsayar.
Wata majiya tace a makon da ya gabata an yi ram da wani da ake zargin mara gaskiya ne a Abuja a kusa da ofishin jakadancin Amurka, yana kokarin yin labe.
Amurka sun yi wa Najeriya taron dangi
A makon jiyan kuma aka samu makamai masu hadari a kofar gidan wani jami’in jakadancin Amurka, daga nan aka gayyato dakarun kasar su zo Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatin Najeriya ba ta ji dadin yadda Amurka ta rika yama-didi da bayanan da ta samu ba, ta sanarwa Duniya a maimakon ta fara ankarar da hukumominta.
Jaridar tace ana zargin kusancin gwamnatin Muhammadu Buhari da kasashen Sin da Rasha wajen sayen makamai shi ya jawo tsamin alakar da ke tsakaninsu.
Jamus, Bulgariya sun yi gargadi
Ofishin jakadancin Jamus ya fitar da jawabi yana kira ga mutanensa su kauracewa zuwa Abuja da wasu garuruwan kewaye idan har hakan ba ya zama dole ba.
Bayanan da ke shafin ma’aikatar kasar wajen Bulgariya ya zo da irin wannan makamancin gargadi. Haka lamarin yake a shafin takwararta watau Denmark.
Ma’aikatar ta bada shawarar a guji zuwa jihohin Adamawa, Borno, Yobe, Gombe, Taraba, Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Sauran jihohin da aka ce mutane suyi hattara da kai masu ziyara sun hada da Filato, Neja, Kogi, Abia, Bayelsa, Delta, Akwa Ibom, Ribas da kuma Kuros Ribas.
Zargi yana kara tabbata
Hakan na zuwa ne bayan labari ya zo a ranar Alhamis cewa Amurka, Ingila, Australiya da Kanada sun ankarar da ‘yan kasarsu kan halin da ake ciki.
Kasashen Amurka, Ingila, Kanada, Australiya da New Zealand sun dauki matsaya daya domin jirgi daya ya dauko su, duk suna tare da jakadancin Amurka.
Asali: Legit.ng