Ministar Tattalin Arziki Ta Jero Sharuda 8 Game da Sababbin Kudin da Za a Buga

Ministar Tattalin Arziki Ta Jero Sharuda 8 Game da Sababbin Kudin da Za a Buga

  • Zainab Shamsuna Ahmed tayi karin bayani bayan an ji sanarwar sake buga sababbin kudi a Najeriya
  • Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi tace bankin CBN da jami’an EFCC za su sa ido a lamarin
  • Gwamnatin tarayya ba ta halattawa bankuna karbar kudin kowa ba illa wanda ya bude asusu a wajensu

Abuja - Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed tayi karin haske game da sababbin kudi da za a buga.

A wani bayani da aka fitar a shafin LinkedIn a ranar Alhamis, an fahimci ba haka nan za a kyale mutane su rika maida kudin hannunsu cikin bankuna ba.

Mai girma Ministar tace za a hukunta duk bankin da ya sabawa ka’idojojin da aka gindaya.

Legit.ng ta bi shafin Ministar tarayyar, ta gane jami’an hukumar EFCC da babban bankin Najeriya za su ika lura da duk kudin da suke shiga asusun jama’a.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Za a rage kudin da ake bugawa

Zainab Shamsuna Ahmed take cewa daga yanzu babban bankin Najeriya watau CBN zai rage adadin takardun kudin da yake bugawa lokaci zuwa lokaci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A farkon shekarar 2023 ake tsammanin Gwamnan CBN zai fitar da sababbin tsare-tsare da za a bi wajen ganin jama’a sun rage yawo da kudi a hannunsu.

Naira
Naira N1000 a Najeriya Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Sharudan da Minista ta jero

1. Dole bankuna su karbi kudi daga hannun mutanen da ake da cikakken bayani a kansu da asusunsu.

2. Dole a zuba dukiya a asusun wadanda suka kawo kudi. Ba za a kai kudi cikin wani asusu ko akawun na dabam ba.

3. CBN da EFCC za su rika bibiyar duk kudin da aka zuba a asusu.

4. Tsofaffin kudi za su daina aiki daga ranar 31 ga watan Junairu 2023.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

5. Wannan zai kasance dama na ganin kudi sun shiga asusu.

6. Hakan zai jawo a komawa fasahar zamani, kuma a rika bude sababbin asusu.

7. CBN ba zai cigaba da buga tsabar kudi da yawa ba. Za a sanar da tsarin takaita tsabar kudi a Junairu.

8. Duk bankunan da suka karbi kudi daga hannun marasa asusu za su gamu da fushin CBN da EFCC.

Me zai faru idan aka buga kudi?

Kun ji labari Gwamnan CBN, Godwin Emefiele yana sa ran buga sababbin Nairori zai magance karancin kudi da ke yawo, ya kauda kazaman takardu.

Masana sun ce idan babban bankin Najeriya ya iya tattara kan kudin da ake da su, ana sa ran a shawo kan yadda farashin kaya suke masifar tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng