Yadda DSS Da Sojojin Amurka Suka Kai Sameme Suka Kama 'Yan Ta'adda' A Wani Gida A Abuja

Yadda DSS Da Sojojin Amurka Suka Kai Sameme Suka Kama 'Yan Ta'adda' A Wani Gida A Abuja

  • Jami'an hukumar yan sandan farin kaya DSS da sojojin Amurka sun kama wasu da ake zargi da hannu a ta'addanci a Abuja
  • Adewale Adenaike, shugaban unguwar rukunin gidaje na phase 3, Trademore Estate, a Abuja ya magantu kan yadda abin ya faru
  • Wannan kamen na zuwa ne kwanaki kadan bayan kasashen waje da suka hada da Amurka da Birtaniya sunyi gargadi kan yiwuwar barazanar tsaro a wasu jihohin Najeriya

FCT Abuja - Adewale Adenaike, shugaban rukunin gidaje na phase 3, Trademore Estate, a Abuja ya bada labarin yadda jami'an DSS da wasu sojojin Amurka suka kama wani da ake zargin dan ta'adda ne a unguwarsa.

Adenaike ya ce jami'an tsaron sun rufe kofofin shiga da fita rukunin gidajen a ranar Monday don hana shige da fice, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

DSS sun yi kame
Yadda DSS Da Sojojin Amurka Suka Kama Yan Ta'adda A Wani Gida A Abuja. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama wadanda ake zargi da ta'addanci a unguwarmu - Adenaike

Shugaba unguwar ya ce an sanar da shi cewa jami'an tsaron suna neman wani mazaunin unguwar da ake zargi da aikata ayyukan 'ta'addanci'.

Ya ce:

"Abin ya faru ranar Litinin. Muna gidajen mu lokacin da aka rufe unguwar. Babu mai shiga ko fita. A matsayin shugaba, na fito in bincika abin da ke faruwa. Na gano cewa samame na da DSS da sojojin Amurka suka kawo, kuma ana zargi, na maimaita zargi, cewa suna neman wani da ake zargi da hannu a ta'addanci. Haka aka ce."
"A yayin da na ke kusantar kofar titin mu, wani jami'in DSS da takunkumin fuska ya tsayar da ni, na ce musu ba zan iya tsayawa ba don mutane suna kira suna neman bayanai don haka suka fada min dalilin zuwansu, lokacin ne na san zargin aikata ta'addanci ne zuwansu.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000

"Saboda jami'an DSS ne da sojojin Amurka, ba abin da zance. Na ce shikenan, su yi abin da za su yi, lokacin da suka gama, kawai mun ga sun tafi da was mutane.
"A yanzu da muke magana, ban da cikakken bayani kan abin da ya faru. Ban san me ya faru ba. Ana ta yada jita-jita amma ni bana yada jita-jita, don haka ban rika baza jita-jitar da na ke ji ba."

Adenaike ya ce jami'an tsaron sun kama wasu mutane a sashin yara wato 'Boys Quaters' na wani gida a unguwar.

Peter Afunanya, kakakin DSS bai amsa sakon da aka aike masa ba na neman karin bayani kan lamarin.

Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani

Kwana uku bayan fitar da gargadin kai harin ta'addanci, wani sabin rahoto ya ce Amurka ta bada shawarwari ga yan Najeriya don kare kansu.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani

Kamar yadda PRNigeria ta rahoto, a cikin shawarar ta baya-bayan nan, Amurka ta ce gargadi matafiya game da ziyartar jihohi 14 cikin 36 na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel