Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000
- Gwamnan babban banki na CBN ya bada sanarwar zai buga sababbin kudin Naira a karshen shekarar nan
- Godwin Emefiele yana sa ran hakan zai magance karancin kudi da ke yawo, ya kauda kazaman takardu
- CBN na zargin akwai wadanda suka boye makudan kudi a hannunsu, wannan zai tilasta masu fitowa da su
Abuja - A ranar Alhamis, Jaridar TheCable ta duba wannan mataki da CBN ya dauka, tayi bayanin yadda hakan za iyi tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.
1. Masu boye kudi sun shiga uku
Jaridar tace daga jin sanarwar Godwin Emefiele, mutanen da suka dankara kudi suka boye, za su fara fito da su har zuwa karshen wa'adin da aka bada.
Temitope Omosuyi yace duk wani mai boye kudi zai kai su banki, wanda kafin yanzu wasu suna amfani da dukiyoyinsu ne ta hanyoyin da ba su kamata ba.
2. Yawon takardun kudi
Gwamnan CBN ya koka cewa 80% na kudin da ke yawo ba su hannun bankuna, ana sa ran idan an yi canjin kudin, takardun Naira su yawaita a bankuna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Tashin farashin kaya
Masana sun ce idan babban bankin Najeriya ya iya tattara kan kudin da ake da su, ana sa ran a shawo kan yadda farashin kaya ke masifar tashi a kasuwanni.
Forbes suna da ra’ayin hakan yana iya rage hauhawar farashi, amma masana irinsu Temitope Omosuyi suna ganin akasin wannan za a gani da farko tukuna.
4. Taba darajar Naira
Rahoton yace wannan matakin buga sababbin manyan takardun kudi zai jawo darajar Naira ta kara tabarbarewa a kasuwar canji, yanzu farashin $1 ya kai N770.
5. Za a kashe kudi
Shugaban kamfanin CPPE, Mada Yusuf yace kudin da za a kashe wajen buga wasu kudi zai taba tattalin arzikin Najeriya, musamman a halin da ake ciki a yau.
Idan aka yi la’akari da abin da za a kashe da ribar da za a samu, Yusuf yana ganin asara za ayi. A shekarar 2020 CBN sun kashe N58.6bn kafin su buga kudi.
Sakin hannun Gwamnan Ribas
Dazu kun ji labarin Jihohin da Nyesom Wike ya ba tallafi a dalilin gobara da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suka yi sun hada da Sokoto da kuma Kaduna.
Duk da arzikin da Legas take da shi, kwanan nan Gwamna Wike ya raba miliyoyi ga matan jami’an gwamnatin jihar Legas da ya je wata ziyara ta musamman.
Asali: Legit.ng