Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja
- Gwamnatocin kasashen Australiya da Kanada sun fadawa mutanensu su guji tafiya zuwa Najeriya
- Kasashen sun yi gargadi cewa tafiya zuwa kasar Afrikan a yanzu yana da hadari sosai ta fuskar tsaro
- An bukaci duk wanda tafiyarsa ba ta zama dole ba, ya jira sai an tabbatar da zaman lafiya a kasar
Abuja - Hukumomin Australiya da Kanada sun gargadi mutanensu a game da yin tafiya zuwa Najeriya a daidai wannan lokaci.
Daily Trust tace wannan gargadi yana zuwa ne kusan kwanaki uku bayan Amurka da Ingila sun gano barazanar rashin tsaro a kasar.
A tsakiyar makon nan aka ji Gwamnatin Australiya ta ba ‘yan kasar ta shawara da su hakura da zuwa kasar Najeriya a halin yanzu.
Ana tsoron ‘yan ta’dda za su iya kai hare-hare, ko ayi garkuwa da mutanen da ke yankin.
Jerin Jihohin Najeriya 14 Da Amurka Ta Ce Matafiya Su Kaurace Musu, Hukumomin Leken Asiri Sunyi Martani
Ya za ayi idan tafiya ta zama dole?
Jawabin yace idan mutum ya ga bukatar yayi watsi da gargadin, ya ziyarci Najeriya, to ya nemi shawarar jami’an tsaron Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Akwai barazanar ta’addaci, garkuwa da mutane, da tashin-tashina a fadin Najeria.
Idan duk da shawararmu, an bukaci ayi tafiya zuwa Najeriya, ayi binciken hanyoyi, a samu shawarar jami’an tsaro kafin a tafi.”
- Gwamnatn Australiya
Gargadin Kanada da Ireland
Gazette tace haka ita ma Kanada ta bada shawara ga mutanenta su guji tafiyar da ba ta zama dole ba zuwa Najeriya, ko da birnin Abuja ne.
Kasar tace babu tabbacin halin tsaron da ake ciki a Najeriya, kuma akwai barazanar fadawa hannun ‘yan ta’adda ko kuwa ‘yan bindiga.
Sauran barazanar da rahoton ya lissafo sun hada da rigingimun gari-da-gari, fashi da makami, garkuwa da mutane da kananan laifuffuka.
Hukumomin kasar Ireland sun ja-kunnen mutane suyi hankali da Najeriya domin za a iya kai hari a shaguna, otel, makarantu ko tashohi.
UK, US sun ce ayi hattara
A baya Gwamnatocin kasashen Amurka da Birtaniyya sun ce akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su aukawa babban birnin Najeriya na Abuja FCT.
Gwamnatin kasar tace masu tunanin zuwa Najeriya su sake tunani domin akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a kewayen garin Abuja.
Asali: Legit.ng