Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

  • Gwamnatin tarayya ta ce yan Najeriya su kwantar da hankulansu game da labarin cewa za'a kai hari Abuja
  • Majiyoyin tsaro sun tabbatar da rahotannin Amurka cewa akwai yan ta'addan Boko Haram a Abuja
  • Gwamnatin Amurka da ta Burtaniya sun gargadi 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kula matuka kan yiwuwar samun hare-hare

Abuja - Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa Najeriya ta fi zaman lafiya yanzu fiye da kowani lokaci a shekarun baya-bayan nan.

Lai ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi a taron UNESCO da ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Talata, rahoton TheCable.

Ya yi martani ne game da gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya tayi na cewa da yiwuwan yan bindiga su kai hari birnin tarayya Abuja.

Ya tuhumci yan jarida da zuzuta lamarin.

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: N200 Zamu Fara Sayar Da Litan Mai, Kungiyar IPMAN

Lai Mohammed
Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed Hoto: TheCable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

"Wasu yan jarida ke yada labaran karya a kafafensu don mutane su duba don su smau kudi."
"Idan da gaske ne an yi gargadin tsaro, na yan kasashen wajen ne mazauna Najeriya."
"Amma kawai yan jarida sun tada hankalin jama'a. An rufe makarantu; an rufe kasuwanni; mutane sun fasa tafiyoyinsu; an rikita rayukan mutane."
"Ina tabbatar muku cewa jami'an tsaronnmu na dukkan mai yiwuwa wajen kare rayukan yan Najeriya da baki mazauna Najeriya."
"Mun kassara yan ta'adda. Mun karya lagon yan bindiga. Kasarmu ta fi zaman yanzu a kwanakin baya-baya nan, sakamakon kokarin jami'an tsaronmu."
"Amma ina tabbatar muku cewa lamarin rashin tsaro ya kare a Najeriya."

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Bayanai sun fara bayyana biyo bayan gargadin da gwamnatin Amurka da Birtaniya sukayi cewa da yuwuwan yan Boko Haram sun kai hari birnin tarayya Abuja nan ba da dadewa ba.

Kara karanta wannan

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Daily Trust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun fara basaja da ayyukan hannu cikin birnin tarayya.

Rahoton yace wasu kwamandojin Boko Haram sun saje da jama'a kuma sun kammala shirin kai munanan hare-hare lokaci guda a Abuja.

Majiyoyi sun bayyana cewa yawancin ofishohin jakadancin kasashen waje dake Najeriya sun san da haka shiyasa suka sanar da yan kasashensu mazauna Najeriya cewa su yi hattara.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel