Buhari ya Ware N23.5bn Domin Sayawa Fadar Aso Rock da su NDLEA Motoci

Buhari ya Ware N23.5bn Domin Sayawa Fadar Aso Rock da su NDLEA Motoci

  • An yi kasafin makudan kudi da nufin sayen sababbin motoci a hukumomi da cibiyoyin gwamnati
  • Akwai fiye da N23bn da aka ware domin motoci daga cikin kasafin kudin da aka gabatar a majalisa
  • Gwamnati ta sake cusa motoci a kundin kasafin kudi bayan an ware Biliyoyi dominsu a shekar nan

Abuja - Gwamnatin tarayya tayi kasafin N23.57bn domin sayen sababbin motoci a shekara mai zuwa. Wannan yana cikin kundin kasafin kudin 2023.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa duk da N22.5bn da gwamnatin tarayya ta ware na sayen motoci a 2022, an sake cusa sayen motoci a sabon kasafin kudi.

Hukumar NDLEA mai farautar miyagun kwayoyi a Najeriya ta na gaba a jerin wadanda za su saye motoci, rahoton yace an warewa hukumar N2bn.

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: N200 Zamu Fara Sayar Da Litan Mai, Kungiyar IPMAN

Baya ga haka sai fadar shugaban kasar Najeriya wanda ake sa ran kashewa N1.9bn a shekarar badi.

Haka zalika sojojin kasan Najeriya za su kashe N1.2bn yayin da hukumar NAFDAC za ta batar da fiye da N900m duk a kan sababbin motocin amfani a badi.

Hukumar da ke binciken hadura a Najeriya za ta saye motocin N736.5m, DIA ta ware N66m, hukumar yi wa malaman lafiya rajista kuma za ta ci N616m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari a mota Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An warewa ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki N565.1m, NPHCDA, NDA, da ofishin SSG za su kashe N540m, N485m sai kuma N497m.

Akwai cibiyar yaki da cin hanci wanda ta ke lissafin sayen sababbin motoci na N413m, sai ma’aikatar ayyuka da gidaje da za a fitarwa N376m a 2023.

A shekara mai zuwa, gidajen yari za su saye sababbin motocin N348m daga kasafin kudi. Wannan rahoto ya zo a jaridar nan ta Aminiya ta ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bankin Musulunci Zata Baiwa Najeriya sama da N786b, Ta Nemi Alfarma Daya

Akwai manyan makarantun gaba da sakandare a garuruwan Filato, Yobe da Ilorin da aka warewa kusan Naira miliyan 900 na sayen sababbin motoci.

Jami’an hukumar NIS masu kula da shige da fice za su samu motocin N276m. An ware makamancin wannan kudi ga ma’aikatar lafiya ta tarayya.

Magance sata a Najeriya

Kun ji labari Atiku Abubakar mai neman takarar shugabancin kasa yana da dabarar takaita matsalar sata da ‘yan siyasa ke tafkawa idan sun samu mukami.

Kola Ologbondiyan yace ‘dan takaran PDP zai yi yadda aka yi da barayin gwamnati a lokacin da Olusegun Obasanjo yake shugabanci tsakanin 1999 da 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel