Hana Yan Najeriya Zuwa Dubai: Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasar UAE

Hana Yan Najeriya Zuwa Dubai: Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasar UAE

  • Manyan Jami'an Gwamnatin Najeriya sun yi Alla-wadai da haramta baiwa yan Najeriya Biza da kasar UAE tayi
  • Minista Hadi Sirika ya fusata yace Dubai ta daina ganin kaman tsoronta ake ji, ko ba ita zamu rayu a Najeriya
  • Kamfanin jirgin saman Emirates ta UAE na bin Najeriya basussukan miliyoyin daloli da ba'a biya ta ba

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana bacin ransa bisa haramtawa yan Najeriya Biza da Gwamnatin kasar UAE tayi.

Emefiele yace Najeriya babbar kasa ce na kasuwanci kuma gwamnatin Dubai ta daina yi mata barazana.

Ya bayyana haka ne yayin zaman da majalisar wakilai ta shirya don tattauna matsalar kudin kamfanonin jiragen kasashen waje $700million da aka ki biyansu, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su

Emefiele yace gwamnati na kokari don ganin an biyasu kudadensu amma abinda gwamnatin Dubai ke yi bai kamata ba.

Dubai
Hana Yan Najeriya Zuwa Dubai: Gwamnatin Tarayya Ta Caccaki Kasar UAE Hoto: Presidency, NIDCOM, House of Reps
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi kuwa Ministan Sufurin Jirgin Sama, Hadi Sirika, yace ko a jikinsa idan gwamnati UAE ta hana yan Najeriya shiga kasarta.

Sirika yace duk da cewa akwai kudaden jiragen sama kasar waje da ba'a biyasu ba, bai kamata kasar Dubai ta rika yiwa yan Najeriya barazana ba.

A cewarsa:

"Idan kuna da matsala da mu, zuwa ya kamata kuyi mu zauna, mu tattauna kuma mu baku abinda ke hannunmu kafin mu gama biya."
"Abinda ke da ban haushi shine barazanar da ake yi. Kowace kasa yanzu sai ta fara yiwa Najeriya barazanar hanata shiga kasar, hana jama'arta Biza."
"Ba zasu yi aiki ba, zasu rufe Legas da Abuja. Su sani fa akwai kasashen da aka yi hannun riga da su kuma sun rayuwa lafiya lau."

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

"Akwai misalai a Asiya, kasashen larabawa, ha da Turai. Ba tsoro muke ji ba. Haka ma gyara zai sa muyi idan muka ji uwar bari."

A riwayar Channels, Sirika ya kara cewa idan aka rufe Najeriya gaba daya, ba komai bane.

Gwamnatin Dubai Ta Fitittiki Yan Najeriya 542 Daga Kasarta, Gwamnatin Najeriya ta kwaso su

Bayan makonni ana tattaunawa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta kwaso yan Najeriya 542 da aka dora daga kasar hadaddiyar daular Larabawa UAE ranar Lahadi.

Yan Najeriyan sun dira tashar jirgin Nnamdi Azikwe cikin jirgin shata da akayi musu ta Max Air.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), wadanda aka kwaso sun hada da maza 79, mata 460, da kananan yara 3

Asali: Legit.ng

Online view pixel